✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokta Sadiya Omar: Dalilin da ya sa na yi da’awa a Ingila

Dokta Sadiya Omar ita ce tsohuwar Amirar kungiyar ‘Yan uwa Mata Musulmi ta Najeriya, kuma Darakta a Cibiyar Nazarin Hausa, sannan malama ce a Jami’ar…

Dokta Sadiya Omar bayan an nada mata sarautar Uwar ’Yan Tarun Nana Asma’uDokta Sadiya Omar ita ce tsohuwar Amirar kungiyar ‘Yan uwa Mata Musulmi ta Najeriya, kuma Darakta a Cibiyar Nazarin Hausa, sannan malama ce a Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato. Ta yi digiri na daya zuwa na uku. Ta kuma yi rubuce-rubuce a kan harkokin rayuwa. Ta yi bayanin yadda ta yi da’awa a Najeriya da kuma Ingila.

Tarihin Rayuwata
Bismillahir Rahmanir Rahim. Sunana Sadiya Omar. An haife ni a kiru da ke Jihar Kano. Ina da shekara uku mahaifina ya rasu. A lokacin da na kai shekara shida aka sanya yayana a makarantar boko, sai na rika kuka sai an sanya ni, domin a gidanmu ba a sanya mata karatun boko, amma da Allah Ya kaddara sai na yi makarantar boko, sai kukan da na yi ya sanya aka hada da ni. Na yi Makarantar Firamare ta dandago, daga nan sai Sakandaren ’Yan mata ta Gwamnati da ke Dala duk a cikin Kano, da na kammala sai na shiga Jami’ar Bayero ta Kano na yi digirina na farko a fannin ilmin koyar da Hausa. Na ci gaba da karatu, inda na yi digiri na biyu a Jami’ar Landan,  na kuma yi digiri na uku a Jami’ar danfodiyo, wanda a yanzu na zama Dokta.
Gwagwarmayar rayuwa
Ban samu wata tangarda duk da tsawon lokaci da na dauka wajen karatu ba, ina yi wa Allah godiya. Ka ga wannan babbar nasarar ce. Baya ga haka, na yi karatun addini sosai, kasancewar a gidanmu dole mutum ya yi karatun addini, ya kasance mai kyakkyawar  tarbiyya. Duk da na yi karatun boko a matakai daban-daban, wannan bai hana ni zama Musulma ta kirki ba. Tun ina karama na fara aikin da’awa har  na je Ingila tsawon shekara 4 a can da ban tsaya ba, a lokacin mukan je babban masallacinsu mu yi da’awa tare da wasu mata na kasashe daban-daban, don ciyar da addini gaba. Da na dawo Sakkwato inda nake zaune sai na kafa kungiyoyin addini daban-daban, daga baya muka samu nasarar bunkasa har muka kafa kungiyar tarayya ta ’yan uwa mata Musulmi wato FOMWAN.  Ni ce Amira ta farko a Jihar Sakkwato, na yi Mataimakiyar Amira ta kasa, daga nan na zama Amira ta kasa.
Bakin ciki a rayuwa
Ranar da mijina ya mutu, kasancewar mun dade muna tare, sai kuma gobarar da ta kone gidana wadda ta yi sanadiyyar mutuwar dana.
Rubuce-rubuce
Na rubuta littafina na farko a kan Mu’azu Hadeja ne, sanannen mawakin nan da ke Jigawa, na yi digirina na uku a kan wakokinsa . Wakokin sun hada da wadanda ya yi ga ’yan uwa da Karuwa da Tutocin Daular Usmaniya. A matsayina ta wacce ke yin aiki a kan fannin neman ilmi na gabatar da makalu da kasidodi kan Daular Usmaniya da kuma Nana Asma’u, daga baya na fahimci babu rubutaccen tarihin gudunmuwar da mashahuran matan Daular Usmaniyya suka bayar kamar na sauran mazan daular.
A yanzu na rubuta wani littafi mai suna Modibbo Kilo. Modibbo Kilo sunan wata mashahuriyar malama a Sakkwato da Kano da Sudan ne, wadda al’ummar wannan lokacin ba su san gudunmuwar da ta bayar ba, ballantana ma har a girmama kwazonta. A littafin akwai bayanin yadda ta yi hijira daga Sakkwato zuwa Saudiyya da kafa.
Dole duk lokacin da ka ce za ka yi bincike kan wani lamari, mutane za su sha bamban da kai a bangaren tunani, kuma ba za su yi magana da kai ba, saboda karancin gaskiya da ake da ita. Na gode Allah da Ya ba ni damar kusaci da Daular Usmaniya ta hanyar aure. Jama’ar hubbaren shehu sun yarda da ni sosai, wadannan su ne suka gajarta mini wahala.
kalubale a fannin rubuce-rubuce
Babban kalubalen da na fuskanta a fannin rubuce-rubucena shi ne, na hakikance ba zan tambayi kowa ya ba ni tallafin kudi ba, don na kafa misali da duk wani mutum da ke son a taimaka masa da wani tallafi na aiki, to ya fara taimakon kansa, saboda mutane sun lalace yanzu kana iya zuwa ka tambayi wani tallafi zai iya tunanin ba gaskiya ka fadi ba, amma in ya ga aikinka da amfaninsa da ingancinsa zai taimake ka daga baya. A wannan aikin da na yi na rubuta littattafai uku ban samu kowane taimako daga kowa ba bayan dangina. Tsorona a wannan aikin da na kwashe shekara shida ina yi ba dare ba rana shi ne, mafiyawan mutanenmu ba su son dabi’ar karatu. Za su ga littafi amma babu ruwansu da dalilin buga shi ballantana har su karanta. Kan haka nake ganin ya dace a samar da dakin karatu ga ’yan firamare da sakandare, sannan malamai su tsare su har sai sun yi karatun yadda ya dace. Ina da rubuce-rubeuce a game da addini da ilmin mata da shi kansa ilmin Hausawa, na gabatar da makalu a kasar Saudiyya da Misira da Sudan da Austiriya da Girka da sauransu, don duk na ba da gudunmuwa ga al’ummata.. 

Gwagwarmayar koyarwa a Jami’a
A gaskiya lokacin da ina yarinya karamar a firamarenmu dukkan darasin da ake yi mana da Hausa ake yi, hakan ke kara sanya mutum ya nakalci harshe. Mafiya girman harsuna a Najeriya Hausa da Ibo da Yarabawa a bisa tsarin kundin kasar nan ya kamata mu ba su muhimmanci, ballantana Hausa da ba a Najeriya kadai ake yinta ba har da wasu kafafen yada labarai na Duniya kamar BBC da Jamus da Amurka da sauransu, duk da haka harshen ba ya samun kulawar da ta dace da shi, wasu dalibai za ka ji suna cewa ‘Hausa yarena ne don haka ba zan karanta ta ba,’ wasu na ganin aba ce mai sauki, yana zaune har sai wadansu sun gwada masa kyawun harshen. Ba yadda za mu ci gaba har sai mun kula da harshenmu mun ba shi matsayi mai daraja, ka je sauran kasashe ka gani.  A lokacin da na je China wurin wani taro, mutanen can ko ka iya Turanci ba za ka yi magana da shi ba, amma mu a nan Najeriya muna nan da tunanin nan na mulkin mallaka cewa idan har ba ka iya Turanci ba, to kana cikin matsala. Ya kamata mu sani naka shi ne naka.
Gwagwarmaya a kungiyoyi
Gaskiya a halin yanzu ina cikin kungiyoyin addinin Musulunci, kuma tun a farko na kafa wata kungiya da ake kira ‘Uwa Mumina’ wadda muke zama mu yi karatu kamar yadda Nana Asama’u ta gudanar a lokacin rayuwarta, ta yi karatu kuma ta karantar, kan haka mu ma muka yi koyi da tarbiyarta, kuma na shiga kungiyar ’yan uwa Musulmi Mata wadda na yi Amira a cikinta, inda har yanzu ina cikinta. Akwai kananan kungiyoyi da nake bayar da gudunmuwa a cikinsu kan fannoni da dama irin sha’anin lafiya da ilmi da sauransu. A zamana kan wannan kujera ta darakta a Cibiyar Nazarin Hausa, na yi makalu da kasidodi da dama kan kungiyoyi daban-daban.   
kasashen da na ziyarta
Gaskiya kam na yi tafiye-tafiye zuwa kasashen Afirka Irinsu Nijar da Misra da Sudan da sauransu. A Turai kuma naje Ingila da Austiriya da Girka da Iran da Faransa da sauransu.
Burina
Burin da nake da shi a rayuwa shi ne, wannan rubutun da na fara in ci gaba da shi, duk wata mace a Daular Usmaniyya da ta bayar da gudunmuwa jama’a ba su san da ita ba sai na fito gudunmuwarta, kamar sauran takwarorinmu maza yanzu haka na samu kusan mata 31 da zan fara aiki a kansu wadanda sun shahara kan ilmi, amma boyayyu ne a wurin al’umma.
Shawara ga mata
Babbar shawarata ga mata ita ce su sani rayuwa idan babu ilmi, sai mutum ya zama kamar dabba,  idan suna so su yi ingantacciyar  rayuwa, to yana da kyawu kwarai da gaske su samu ilmi, ilimi na muhimmanci ga mata, idann sun samu kamar al’umma ce ta samu. Kuma su sani rayuwa ba ta da tabbas idan suka yi alheri za su samu abin da suke bukata.