✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokta Maude Gwadabe ya zama Sabon Shugaban Aminiya

Tsohon malamin aikin jarida zai jagoranci Sabon Sashen Aminiya da aka inganta.

Rukunin Kamfanonin Media Trust, mamallaka jaridun Daily Trust, Aminiya da kuma Trust TV da Trust Radio, ya nada Dokta Maude Rabiu Gwadabe a matsayin Shugaban Sashen Hausa da aka kara ingantawa.

Dokta Maude Gwadabe ne zai jagoraci bangaren jarida da kafofin yada labarai na zamani na Aminiya domin ci gaba da tafiya daidai da zamani tare da bullo da sabbin tsare-tsare don isa ga karin masu amfani da harshen Hausa.

“Nadin nasa ya yi daidai da manufar kamfanin na ganin Aminiya ta zama cikakkiyar kafar yada labarai ta zamani, wadda ke isa ga matasa da kananan al’ummomi da ke amfani da harshen Hausa a Najeriya da sauran sassan duniya,” in ji kamfanin.

Sanarwar da Babban Edita kuma Babban Daraktan Gudanarwa a bangaren Aikin Jarida da Fasahar Zamani na kamfanin, Naziru Mika’ilu Abubakar, ya fitar ranar Lahadi ta ce Dokta Maude Rabiu Gwadabe zai fara aiki nan take.

Babban Editan ya ce, “Muna farin ciki da zuwan Dokta Gwadabe, musamman a wannan lokaci da muke kokarin fadada kafofinmu na yada labarai domin isa ga sabbin al’ummomi.”

Kwarewar Dokta Gwadabe

Baya ga shaidar digirin farko da kuma digirgir a fannin aikin jarida, Dokta Maude yana da shaidar digiri na biyu a fannin Nazarin Sadarwar Siyasa daga Jami’ar Leeds da ke kasar Birtaniya.

Maude Rabiu Gwadabe
Dokta Maude Rabiu Gwadabe

Sabon Shugaban Sashen Hausan tsohon dan jarida ne a Sashen Hausa na BBC a bangaren rediyo da kafofin yada labarai na zamani.

Tsohon malami ne a Sashen Koyar da Aikin Jarida na Jami’ar Bayero ta Kano, inda ya ajiye aiki a shekarar 2019.

Ya yi aiki da hukumomin kasashen duniya irin su iMedia da Hukumar Kula da Cigaban Kasashe ta gwamnatin Amurka (DFID) da kuma Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) a matsayin kwararren mai ba da horo da shawarwari kan aikin jarida.

Tsohon edita ne a gidan rediyon Freedom da ke Kano, shi ya assasa kafar yada labarai ta intanet mai suna Kano Focus, sannan shi ne shugaban farko na gidan rediyon Ndarason da ke Maiduguri, Jihar Borno.