Littattafan da ya wallafa:
Littafinsa na farko da ya bayyana a kasuwa shi ne ‘Wane ne Alkali?’ (1992) duk da cewa ba shi ne littafin da ya fara rubutawa ba, yana bayani ne a kan siffosin da alkali ya kamata ya siffatu da su. Bayan shi sai littafinsa na biyu, ‘Kai Wane ne a kotu?’ (2000) inda yake bayyana wa mai karatu siffofin mai kara da wanda ake kara da kuma na mai ba da shaida.
Littafinsa na uku da ya bayyana a kasuwa wanda kuma shi ne na farko da ya rubuta yana dan shekara 11, shi ne littafin ‘Mu San Sunna a Saukake’ littafi na 1 mai kunshe da hadisai 100 da fassararsu cikin harshen Hausa. Sai kuma littafin da ya yi kan shu’umammen tsibirin nan mai cike da hatsarurruka mai suna ‘Bermuda Triangle da Hatsarurrukansa’ (2000).
Wani littafi da ya fita daban daga cikin littattafansa, shi ne wanda ya yi a kan rayuwar aljanu tun daga haihuwarsu har zuwa mutuwarsu mai suna ‘Halittar Aljanu, Rayuwa Zuwa Mutuwa’ shi ne littafinsa na hudu da ya rubuta (2001). Da yawan mutane kan dauka cewa aljanu ba sa mutuwa, amma marubucin ya yi kokari, ta hanyar fito da hujjoji don kokarin gamsar da mai karatu cewa lallai fa aljanu, a matsayinsu na halitta, su ma suna mutuwa. A cikin littafin ne ya yi bayani kan aljanu cewa “Da yawa mutane sun dauka aljannu munana ne a halittarsu, saboda muninsu ma, wanda ya gan su, mutuwa zai yi. Wani mawaki, marigayi dan Anace yana cewa: “…kowagga aljani bai kwana”. A gaskiya ba haka ba ne. akwai kyawawa cikinsu akwai kuma munana. Wasu ma ai daukar su aka yi cewa “Iska/Iskoki” ne. E, Iskoki ne amma masu rai da kuma jikin da ba kowa ke iya riskarshi ba. To ka ji….”
Ya yi bayani kan yanayin aljanu, haihuwarsu, auratayyarsu, ilminsu, dabi’u da mu’amalarsu, tafiyarsu da kuma al’adarsu.
Sauran littattafan marubucin sun hada da; Mafarki; Fassararsa da bayaninsa, Tare da Manzo Koda Yaushe, Mu San Sunna a Saukake, littafi na biyu.
Ba a harshen Hausa kawai marubucin yake rubutu ba, domin akwai littattafai da wakoki da ya rubuta cikin harshen larabci da kuma turanci. Daga cikin littattafansa na larabaci akwai sharhin Nuzhatul Asiri da wani littafi mai suna ‘Ahmad Shauki, Thakafatuhu Wattijahuhul Adabiy da kuma littafin koyon haruffan larabci mai suna ‘Haruffan Larabci na 1,2,3 har zuwa na 4. Daga ciki akwai Raino a Shari’ar Musulunci (2002) sai mukaloli daban-daban da ya rubuta a kan harshe da adabi.
A bangaren turanci kuwa, ya rubuta littafi mai suna ‘Concept Negritude, a Guide for Writers and Critics da kuma sunayen Allah (Asma’ullahil Husna) cikin harshen turanci.
Wakokinsa
Duk da cewa suna da alaka da juna, amma ba kowane marubucin labarai ne ya iya rubuta wakoki ba, kamar yadda ba kowane mawaki ne ya iya rubuta labarai ba, amma idan ka kalli Dakta Lawal Sule Abdullahi sai ka rasa a wanne ne ma ya fi kwarewa! A bangaren wakoki kam, babu shakka bahari ne shi, domin kuwa hatta littafin Aruli, littafin da ke dauke da ma’aunan wakoki, ya dauko shi ya fassara shi da Hausa cikin wake don saukaka wa dalibai da masu nazari wajen fahimtarsa wanda a halin yanzu ake amfani da shi a jami’a wajen koyar da dalibai bayan ya kai wa marigayi Farfesa Kabir Galadanci na jami’ar Bayero ya sa masa albarka.
A cikinsa ne yake cewa:
dawili Karin farko kafa ce dawiliya guda sai biyu ninka su tilas ka hautsina. Wakarsa ta farko ta yabon Annabi ce, wacce ya yi ta tun yana makarantar sakandare da harshen larabci. Ya yi waka a kan jarabawa da irin wahalhalun da ke tattare da jarabawa da tanadin da ya kamata dan makaranta ya yi. Sai wata mai suna ‘Rayuwar Kudu’ inda a ciki yake bayyana irin yadda rayuwar ‘yan kudu take. Ga kadan daga cikin abinda yake cewa:
Rayuwar kudu ba dadi ka ga yara na badadi.
Ko ina da ido a kudi ba ibada sai ta kidi.
Sai wata waka da ya yi mai suna Himma, wacce ya yi domin karfafa matasa. Fasihin mawakin, da yai la’akari da irin rukunin wadanda zai yi wa wakar, sai ya yi ta da Ingausa (Haduwar kalmomin Ingilishi da Hausa) sai dai shi ya kira shi da Turausa (wato Turanci da Hausa).
Ga kadan daga cikin abin da yake fadi a wakar:
Ba ni kin yin good mobement in missing din enjoyment
Permanent nai fulfilments don rashin good agreement Daga cikin fitattun wakokinsa akwai ‘Cukumurdi’ wacce asali ya yi ta ne da larabci (Inda ya ba ta suna Ash-shakawa Ilallah) amma saboda ganin irin karbuwar da ta yi har a jami’o’in kasashen waje da na cikin gida Najeriya sai ya mayar da ita zuwa hausa.
Cukumurdi (cukurkudewa, hargitsewa da kuma cakuduwar al’amura), waka ce mai baituka dari wacce ya siffanta rayuwar ‘yan Najeriya ta fuskar hargitsewar al’amura ta fuskar tattalin arziki da fuskar zamantakewa da batun cin hanci da rashawa da sauransu, inda ya kawo matsalolin da ke addabar wannan kasa da kuma mafita. An taba kawo cikakkiyar wannan waka a wannan shafi na jaridar Aminiya.
A halin yanzu malamin na kan rubuta wata mukala wacce zai gabatar da ita a jami’a mai suna ‘Waka a Gadon Fida’ don koya wa dalibai irin yadda ake nazarin harshen Hausa a waka da yadda ake nazarin littafan Hausa da yadda ake warware ma’anoni da hadafi. A cikin mukalar, malamin ya dauki daya ne daga cikin wakokin marigayi Alhaji Dakta Mamman Shata ya dora ta a gadon fida inda ya fitar da hanji da huhu da hanta da mazawuri a gefe guda, sannan ya ware fata daban.
Takaicinsa da Halin da Rubutun Hausa yake fuskanta da kuma shawarwarinsa ga marubuta
A cikin wata tattaunwa da ya yi da wakilinmu, malamin ya bayyana takaicinsa da irin yadda ba ma adabin Hausa ba, shi kansa harshen na fuskantar matsaloli masu yawa daga masu amfani da ita musamman wajen rubuce-rubuce a jaridu da littattafai da kuma karantata a gidajen rediyo da talabijin.
Ga kadan daga abin da yake cewa, “Matsalar da aka samu ita ce su ‘yan bokon farko sun rungumi harshen turanci da kyau kuma sun samu kwarewa a kanta amma ‘yan bokon baya-baya kuma bayan sun saki nasu sai kuma suka kasa maida hankali a kan turancin sai suka yi ba wan, ba wan. Ba su iya bai wa wancan muhimmanci ba, ga shi kuma sun saki wannan…”
Matsala ta biyu da ya ambata ita ce ta rashin samar da tsayayyar kasuwa ga marubuta littattafai ta yadda mafi yawansu asara su ke tafkawa, domin ko mutum ya yi littafi na 1 da wuya kudin su dawo ballantana ya yi na 2.
Littattafan da malamin ya kira ‘Gobe Kasuwa’ na daga cikin irin littattafan da suke hada haruffa da kalma ko kalma da kalma fada, saboda rashin sanin ka’idojin rubutu domin damuwar irin wadannan marubutan shi ne alla-alla suke su rubuta abin da ke cikin zuciyarsu a je kasuwa a sayar ba tare da zuwa wajen wani kwararre a kan harshen don dubawa da yin wasu ‘yan gyare-gyare ba.
Daga cikin irin kura-kuran da malamin ya ambata da ya shafi ‘yan jarida shi ne fassara, inda ya kawo misali da wani labari da ya saurara kwanan nan ana karanatawa a wani gidan rediyo sai ya ji mai karanto labarin na cewa “…shugaban kasar ya yarda zai ga kowa amma ta hanyar kamara (abin daukar hoto)” ka ga wannan bai san harshen turancin da yake fassarawa ba, bai kuma san harshen hausar da yake fassarawa zuwa gare shi ba, domin jumlar da yake fassarawa ita ce “I want to see you in camera” wanda abin da wannan shugaba yake nufi shi ne yana so ya gana da kowa a kebe.
Malamin ya yi kira ga marubuta da su sani akwai masana, don haka in sun yi rubutu su rika kaiwa ana duba musu domin bai wa komai hakkinsa.
Malamin ya ba da shawara ga masu gabatar da shirye-shirye musamman a gidajen rediyo da kullum sai dai su rika gayyato ‘Jaruman’ shirin fim da su rika yin kokari suna gayyato marubuta domin rubutu shi ne ya fi zama dahir wanda yana nan har bayan shekara dubu, ba wai kullum a ce sabon fim ya fito ko sabon waka ya fito ba, inda ya bukaci kafafen yada labarai da su rika gayyato marubuci idan ya yi wani sabon littafi su yi hira da shi ya yi bayani kan irin abubuwan da littafin ya kunsa da sauransu, domin in an ba albasa ruwa, to yalo ma ya kamata a ba shi.
Sannan a karshe ya yi kira ga gwamnati da ta rika tallafa wa marubuta wajen fitar da littattafansu da kuma wajen adana su a dakunan karatu ta yadda ba za su bace ba, inda ya koka da cewa hatta jaridu da ake adanawa ma yanzu a dakunan karatu ba ko ina ake samunsu ba.