Daya daga cikin dattawan Najeriya kuma dan Majalisar Tarayya a Jamhuriyya ta biyu, Dokta Junaidu Mohammed ya koma ga Mahaliccinsa.
Dansa, Sulaiman Mohammed ne ya inganta rahoton mutuwar a wata tattaunawa da ya yi da Aminiya a daren jiya na Alhamis.
- Sheikh Gumi ya shawo kan ’yan bindigar Neja
- ’Yar shekara 12 ta kafa tarihin yin iyo a teku na kilomita 36
- ‘Abin da ke kawo rikicin kabilanci a Najeriya’
Tsohon shugaban marasa rinjaye a zauren Majalisar Wakilai ta Najeriya ya rasu da misalin karfe 10 na daren ranar Alhamis a gidansa da ke Jihar Kano bayan ya yi jinya ta tsawon kwanaki uku.
Marigayin wanda ya shahara a jam’iyyarsa ta PRP (Peoples Redemption Party) ya kuma kasance sananne a fagen bayyana ra’ayi game da zamantakewar al’umma.
Ya samu horo kan aikin Likitanci a Tarayyar Soviet inda daga bisani ya samu kwarewa a kan tiyatar kwakwalwa a Kasar Birtaniya.
A yayin da Aminiya ta ziyarci gidansa da misalin karfe 11.00 na dare, mutane da dama sun yi ta tururuwa domin bayyana alhininsu.
Dokta Junaidu wanda ya shafe shekara 73 a doron kasa, za a yi jana’izarsa a yau Juma’a bisa tanadin addinin Islama kamar yadda dansa ya shaida wa wakilinmu.
Marigayi Junaidu na daya daga cikin Dattawan Arewa da suka shahara wajen sukar gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.