✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dokta Ahmad Shehu: Daga makarantar makiyaya zuwa malamin jami’a

Malamin wanda yanzu karamin farfesa ne a Jami’ar Jihar Kaduna ya bayyana wa Aminiya irin dauki-ba-dadin da ya yi da danginsa kafin ya kai matsayin…

Dokta Ahmad Shehu da wadansu suka fi sani da Pullo Jada, daya ne daga cikin daliban makarantun ’ya’yan makiyaya (Nomadic) da ya sha gwagwarmaya wajen ganin ya samu ilimin zamani.

Malamin wanda yanzu karamin farfesa ne a Jami’ar Jihar Kaduna ya bayyana wa Aminiya irin dauki-ba-dadin da ya yi da danginsa kafin ya kai matsayin da yake kai a yanzu.

Kuma ya bayyana yadda za a iya shawo kan ta’asar masu garkuwa da mutane.

Aminiya: Mene ne tarihinka a takaice?

Sunana Ahmad Shehu an haife ni a tsakanin kananan hukumomin Jada da Ganye a wata rugar Fulani da ake kira Mamugal. A yanzu rugar ta zama kauye mutane sun karu.

An haife ni a Oktoban 1985, a nan na taso na yi yawancin rayuwata har na girma. Iyaye da kakannina Fulani ne makiyaya masu kaura daga wannan wuri zuwa waccan.

Kakannina sun taso ne daga bangaren Difa da Maini a Jamhuriyar Nijar, sun yi rayuwa a wurare da dama a matsayinsu na makiyaya. Sai dai sun fi zama a yankin Yobe a garuruwan Gaidam da Gashuwa. Daga bisani sun tafi Kudu yin kiwo har suka kai Mambila.

Zaman bai yiwu ba suka shiga Kamaru kafin su sake dawowa Najeriya. A nan yankin aka haife mu, mahaifinmu ya ce yawon ya isa haka sai muka ci gaba da karatun addini.

Idan na fahimce ka iyayenku ba su yi karatun boko ba ke nan?

Iyayenmu musamman muhaifinmu Allah Ya saka masu da alheri, shi ne ya lura cewa karatun boko ya zama dole, kuma ya zo daidai da lokacin da aka fito da Hukumar Kula da Ilimin ’Ya’yan Makiyaya a 1989, sai ya roka aka ba shi makarantar lokacin ana Karamar Hukumar Ganye.

Da aka kawo makarantar ba mu da yawa saboda ruga ce ta Fulani amma duk da haka aka samu yara aka fara karatu a karkashin wata bishiyar mangoro a gaban gidanmu.

A nan muka fara da shekara ta kare aka samu wani ajin muka bar karkashin mangoron har yanzu na nan a rugar muka koma wata rumfa.

A rumfar dattijai ke haduwa da rana kuma a nan suke cin abinci, sai suka bar mana muka mayar da wurin aji da safe, tunda ba sa zama da safe, idan muka tashi da rana lokacin sun dawo daga hidindimunsu sai su yi zamansu a rumfar.

Da muka shekara uku aka samu aji uku sai aka koma da mu karkashin wata bishiyar kadanya da ke kofar masallacinmu na rugar, aji biyu suka dawo rumfar, aji daya na karkashin mangoron.

Ana wurin ne aka rika neman fili domin daga cikin kalubalen da ke damun Fulani makiyaya akwai rashin wurin zama nasu duk inda suka zauna sai a ce matsa namu ne, ko tashi nan na kakana ne da sauransu.

Hakan ya sa aka yi ta zuwa kotu har mahaifinmu ya samu wani fili a kusa da gidanmu.

Har an yi ajujuwa sai wani mutum da ke garin Jada ya ce filinsa ne aka shiga shari’a ya yi nasara tunda su ne ’yan kasa.

Daga nan muka samu wani fili a kasa da kilomita daya daga inda garken mahaifinmu yake.

Sai aka yi rumfuna aka fara karatu, amma Allah cikin hukimarSa wadansu mutanen da suke ganin bai kamata ba muna baki a ce muna da makaranta ba suka biyo dare suka kona rumfunan.

To, babu zabi sai muka sake dawowa karkashin bishiyoyin da muke karatu.

An yi shari’a ta shekaru sai aka samu wuri a kan duwatsu inda ba za a iya shuka ba aka gina dakin laka muka kara wa firamare.

Yanzu wurin ya ci gaba sosai an gina ajujuwa shida. An gina karamar sakandare, abubuwa sun bunkasa.

A haka na yi firamare, muna da yawa da aka dauka amma sha’anin mutanen ruga, yara suna tafiya kiwo kuma karatu abu ne mai daukar lokaci, don haka mu shida ne kacal muka kammala firamare a cikin sama da 100.

Da muka kammala sai aka kai ni karamar sakandare a Jada. Bayan kammala zangon karatu na daya sai aka mayar da mu makarantar je-ka-ka-dawo da ke kauyen Dashel, kamar kilomita uku daga rugarmu, ta yadda za mu iya kiwo mu yi karatu don da safe idan an tafi hutun rabin lokaci mai kiwo zai tafi.

Ni da kanina da yanzu likita ne muna karbebeniyar kiwo. Muna kiran haka da Fulatanci da Gurnaje. Ka yi kwana biyar ko mako wannan ya yi kwana biyar ko mako.

Ranar da zan yi kiwo da an je hutun rabin lokaci sai in tafi in kiwona, shi ma haka. A haka muka gama firamare.

Muna sakandare a Jada ne aka samu wani shiri na Hukumar DFID ta gwamnatin Ingila inda aka zabi ’ya’yan Fulani makiyaya da suke da kwazo a Jihar Adamawa na samu lamba ta biyu, aka dauke ni aka kawo ni Kwalejin Koyar da Malanta da ke Yola, a nan muka yi shekara daya da rabi zuwa biyu aka horar da mu.

Daga nan muka rubuta jarrabawar takardar malanta mai daraja ta biyu a NTI na ci darussa biyar.

Sai na shiga sakandare a 1997, wannan tsari na DFID ya zo 1998 don haka zuwa 1999 muka kammala.

Ke nan maimakon shekara shida a sakandare biyu ka yi?

Eh shekara biyu zuwa uku na yi, a lokacin da na kammala sakandare sa’annina suna karamar sakandare aji uku.

Mu 30 aka kai kwalejin ta Yola shiri, ne na musamman don samar da malaman makarantun makiyaya.

Bayan mun kammala, dama tsarin shi ne a koya wa ’ya’yan makiyaya ilimi su koma gida su koyar da ’ya’yan makiyaya a makarantun da ke ruga.

Saboda malaman da suke zuwa daga birane ba za su iya zama a rugagen Fulani ba.

Da muka koma na koyar a makarantun makiyaya na tsawon shekara 11, na zama malami ina dan shekara 13. Na koyar a firamarenmu ta Mamugal, wadda ta bunkasa, muna da yaran da suka zama likitoci saboda an mayar da kai gida kuma kai dan uwansu ne.

Ka san yawancinsu kannenka ne za ka ladabtar da su babu mai cewa don me.

Daga baya na nemi zuwa karatu a jami’a, na samu amma aka ce wai na yi kankanta saboda a lokacin ina dan shekara 15 ne.

Saboda haka sai na tafi Kwalejin Ilimi ta Yola na yi NCE, na koma na dan koyar kafin in tafi Jami’ar Maiduguri a shekarar 2006 wadda na kammala a shekarar 2009, inda na karanta Ingilishi da Fulatanci na fito da Digiri Mai Daraja ta Daya (First Class), wannan ne ya kara min kaimi wajen kara karatu.

Na yi hidimar kasa a Jami’ar Bayero da ke Kano bayan na gama na koma gida ina neman aiki.

Na samu ayyuka da dama na koyarwa a Jami’ar Bauchi da Jami’ar Bayero da Kwalejin Ilimi ta Yola, sai na tafi Jami’ar Bayero a shekarar 2012, daga nan na wuce kasar Malesiya na yi digiri na biyu a fannin harsuna (Lingustics) a Jami’ar Malaya, na samu sakamako mai kyau na dawo Bayero na ci gaba da koyarwa a shekarar 2014 zuwa 2016.

A shekarar 2017 na tafi kasar Poland na yi digiri na uku, karatun shekara hudu ne amma Allah Ya taimaka na kammala a shekara biyu.

Na dawo Bayero na shekara daya daga nan na koma Jami’ar Amurka a Najeriya (AUN) da ke Yola.

A nan Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) aka mayar da ni karamin farfesa (Associate Professor) inda na dawo da aiki.

Ko akwai kalubalen da ka fuskanta kafin ka kawo inda kake a matsayinka na makiyayi?

Ai rayuwar ma gaba dayanta kalubale ce, kawai taimakon Allah ne, amma babu abin da mutum zai same shi a garabasa.

Na farko ni Bafulatani ne makiyayi, a yanzu haka akwai ’ya’yan kawunaina da suke irin waccan rayuwa ta makiyaya.

Ni ne na farko a zuriyata da ya yi karatun boko don na addini kowa ya san Fulani masana addini ne.

Kuma na samu digirin farko kuma ina jin a duk tsarin ilimin ’ya’yan makiyaya a Najeriya da aka yi shekara 30 da suka wuce ni ne na farko da na samu digiri na uku (PhD) a duk kasar nan.

Saboda haka wannan ya nuna cewa hanyar da kai ne ka fara bin ta, ka san daji ne kawai.

Kana dai tafiya ce kawai babu mai nuna maka ka bi can ko ka bi nan, ko me yi maka gyara a mutanen da suke kusa da kai.

Kuma da na yi kokarin zuwa jami’a ’yan uwana gaba daya ba wanda ya goyi bayana, suna ganin bata lokaci ne hatta maza wadanda suka dade da dan wayewa suna kasuwanci tunaninsu shi ne tunda ina da NCE kuma ni malamin makaranta ne me zan yi da wani satifiket.

Na biyu idan ma kudi zan nema ai ba a samun kudi a karatu tunda ga malaman nan ko kudin aski ba su da shi.

A lokacin mahaifinmu ya rasu saboda haka ba ni da kwarin gwiwa, haka nake tafiya a kan abin da na yanke wa kaina kurum.

Bayan haka ga rashin kudi domin dukkan ’yan uwa maza da mata yawanci ba sa ganin alfanun abin.

Da ka ce za ka yi ana ganin barna ce, mahaifinmu ya bar mu da shanu amma kusan kowa nasa sun kare saboda ana sayarwa don biyan bukata.

Saboda haka ina da sauran daya, to a ranar da na ce zan sayar da dayar don tafiya jami’a kuka aka rika yi. Yaya za a yi mutum ya sayar da saniyarsa ta karshe ya ce zai tafi makaranta?

Amma abu ne da na sa a zuciyata cewa zan yi, don haka na sayar da ita na tafi kuma aka bata sosai, akwai ma wadanda aka daina magana uwa daya uba daya, saboda na yi taurin kai na ce sai na je Maiduguri karatu, za su ga yadda za a yi in yi karatun.

Wadanda suka taimaka min a cikinsu mutum biyu ne kawai, wani dan kawuna Yahaya, ya taimaka min da Naira dubu 1500, ’yan dari biyar-biyar har yanzu ina tunawa.

Sai babban yayanmu da muka hada uwa da shi, duk ranar da zan koma zai ba ni kudin mota kadai.

A lokacin Naira 2,000 ke kai ni Maiduguri, don haka zai ba ni Naira 2,000.

Sannan na yi fama da rashin gata saboda kana tunanin idan wani abu ya taso na sayen takardu ba ka da wanda za ka kira ka fada masa.

Sannan ga rashin wanda zai sa ka a kan hanya ko ya nuna maka haske kan abin da za ka karanta a makarantar.

Ko da zan nemi jami’ar ban taba zuwa Yola ba kuma a lokacin babu intanet ko ba yawa.

Saboda haka da na sayi takarda na cika haka na shiga mota na tafi Maiduguri ba tare da na san inda zan je ba.

Da na isa na nemi ’yan Jada a Maiduguri na shiga makaranta na nemi inda sashenmu yake na samu wani Malam Adamu yanzu yana FCE na ba shi takarduna na ce masa ina neman jami’a.

Zan iya cewa wannan ne ya sa mahaifiyarmu ta samu hawan jini saboda ba ta san inda nake ba.

Na samu gurbin shiga jami’a ce a lokacin na je kauyen Dashin da wayar abokina sai ga tes an ce na samu shiga jami’a, kamar wasa na je na fara karatu.

Kalubalen makaranta ya fi yawa amma idan ka yi niyyar yin abu kuma Allah Ya nufa za ka yi to za a rika samun dalilin da za su dora ka a kan hanya.

Duk inda na kai idan na ga kamar ba zan iya wucewa ba sai Allah Ya turo min wani wanda zai iya riko da hannuna in wuce.

Kamar a Maiduguri, Allah Ya hada ni da wani da ya zama kamar uba a gare ni, wato Dokta Abubakar Girie shi ya rike ni ya cire min maraici.

Malami ne a wurin zai kai ni gidansa idan ina da matsala zai ba ni kudi, idan ba ni da waya zai saya min muna tare ba dare ba rana.

Haka ya yi min har na gama makaranta aka dawo gida.

Sha’anin yadda ake kallon karatu a Najeriya na san sabon kalubale za a shiga don sai aka ce min mun ji ka je ka yi digiri ka dawo, sai kuma me?

Ka ga dai malamin firamare ne ni albashina lokacin Naira dubu shida.

Idan na wuce sai ka ji an ce dube shi da saniyarsa ce take nan a yanzu da sun zama nawa.

Idan ka sa wando jeans sai a ce dube shi dan iska. Idan ka wuce a zage ka wani lokaci a fada maka magana kai-tsaye.

Wani kalubalen shi ne mahaifinmu da ya nemi a kafa makarantar shekaru ya yi ana kai shi kotu a kan wurin da zai kafa makarantar.

Amma shi bai yi karatun boko ba ko?

A’a bai yi ba kishi ne kurum na ganin za a yi karatun. Saboda haka ya je kotu ya sayar da shanunsa a kan a samu filin yin makarantar saboda bakunta.

Ashe kafa makarantar ma kalubale ne bare mu da muka bude hanyar a kasa baki daya.

Muna cikin wadanda suka tsaga wadannan hijaban matsaloli muka yi karatu.

Idan mutum ya ce zai tuna matsalolin da aka fuskanta da shekarunka sai ka ga kana hawaye.

Ka ce akwai dan uwanka likita, tare kuka yi karatun?

Eh, kanina ne amma ba shakiki ba. Lokaci daya muka yi, ina aji uku a jami’a na koma gida na dauko shi saboda ya dade da kammala sakandare kuma yana da kwazo sosai, amma babu damar tafiya makaranta.

Kuma akwai wani dan kawuna da ya taimaka mana da Naira dubu shida a lokacin, sai na dauke shi muka koma Maiduguri.

A can ya yi rimidiyal ya samu sakamakon mai kyau aka ba shi sashin koyan likitanci a nan, na kammala karatuna na bar shi a Maiduguri.

Mu muke daukar nauyin kanmu sai dai Allah Ya hada mu da mutanen da suke taimaka mana. Sai noman da muke yi da kuma koyarwa da sauransu.

Ka je Malesiya da Poland karatu, ga shi kana aiki, shin ’yan uwanka sun fahimci amfanin karatun?

 (Dariya). Ai ka san dan Adam bai yarda da badini ba, dan Adam ya fi yarda da zahirin abin da yake gani.

A yanzu za su ga cewa ashe dai abin da nake yi ya fi kiwo domin za a kira ka Dokta da sauransu. Amma har yanzu ba a yi wa karatu kyakkyawar fahimta ba.

A cikin Fulanin daji idan aka yi maganar boko a Najeriya ta Arewa Fulanin za a kira a bokon domin Hausawa ba su yi bokon Fulani ba.

Amma idan aka ce Fulani makiyaya ko Hausawa na karkara ko Barebarin karkara su ake magana.

Abin ba a kabilar yake ba a tsarin rayuwa yake, domin tunanin da Bafulatanin daji yake yi wa karatun boko shi ne Bahaushen karkara yake masa.

Wadanda suke da dan dama-damar fahimta ne ke yi wa karatun kallon a yi karatu a yi kudi a kuma ji dadi.

Wannan an waye ke nan amma akwai wadanda suke ganin Yahudanci ne da bata lokaci domin ba tsarin addini ba ne.

Allah Ya jikan wani Baffanmu idan na je wurinsa sai ya ce ya ga babanmu na son ya bata ni.

‘Ka dawo gidana, ni abin da nake so ka zama, shi ne ladani a masallaci (dariya).’

Ba karamin abu ba ne zama ladani domin a yanzu haka mutum bai fi karfin zama ladani ba, saboda abin da ladani yake samu wurin Allah ba za ka samu komai ba a boko. Ko ba haka ba.

Shi iya hangensa ke nan saboda ganin yadda na iya karatun Kur’ani domin malaminmu ne na Kur’ani da hadda da yadda nake kusa da su manya duk da cewa ni yaro ne.

Idan na dawo kiwo babu inda nake zama sai inda manya suke, tare muke Sallah wani lokaci in ja Sallar.

Sai ya ce, ‘Idan na yi karatun boko zan iya sayar da iyayena domin karatun ’yan wuta ne, amma tunda Muhammadiyar nan ka iya, ka dawo gidana ka zama ladani har ka zama liman nan gaba in Allah Ya yarda.’

Kafin rasuwarsa abubuwa sun canja domin mun girma a lokacin yana kuka da hawayensa cewa ’ya’yansa su bi mu su yi karatun boko.

Saboda haka kallon da ake yi wa ilimi har yanzu ba kallo ne na daidai ba. Ba a yi wa karatun kallon wani bangare ne na rayuwa idan babu shi akwai matsala ko mai kake da shi.

Ana son ka yi karatun ne saboda ka iya rayuwa ba wai ka yi aiki ko ka zama lakcara ko ma’aikacin banki ba.

Kana bukatar ilimi ne saboda ka iya rayuwa in kasuwanci za ka yi ko noma za ka yi don idonka ya bude. Za ka yi karatu da rubutu ka san mene ne kiwon lafiya da sauransu, shi ne amfanin karatu.

Ka yarda matsalolin da Fulani ke fuskanta a yanzu a dazuzzuka suna da alaka da rashin ilimin boko?

Dari bisa dari na yarda, domin babu wanda yake bukatar a gaya masa haka.

Na san mai ilimi na iya zama dan ta’adda amma ta’addancin mai ilimi, ilimi zai magance shi.

Su jahilai wadanda babu wani abu na rayuwa da za su rayu da shi ba abin da suka sani a nan duniya ban da shanunsu.

Idan da za ka kora garken shanun Fulani idan su goma ne a zuriyarsu ka kure rayuwarsu ce gaba daya, domin babu wani abu da za su iya yi, saboda babu wani abu da suka taso suna yi.

Ni da ’yan uwana da wadanda muke tare a garinmu a yanzu ba kamarsu ba ne tunda garin ya girma sosai, a yanzu muna gina asibiti mun gina makarantunmu yaranmu suna karatu da kasuwanci.

Idan kana da shanu suka shekara ba ka gan su ba, zai yi wuya hankalinka ya kwanta, a yanzu na shekara kusan uku ban ga shanuna ba.

Alakarka da su shi ne a kai kasuwa a sayar a aiko maka da ’yan canjin.