✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya fice daga gidan gwamnatin Ribas 

Gwamnan da aka dakatar ya fice daga fadar gwamnatin jihar da sanyin safiyar Laraba.

Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Similanayi Fubara, ya fice Fadar Gwamnatin Jihar da ke Fatakwal.

Majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa Fubara ya fice daga Fadar Gwamnatin da safiyar Laraba, a daidai lokacin da sabon Shugaban Riƙn Ƙwarya, Admiral Ekwe Ibas (mai ritaya), ke shirin karɓar ragamar mulki.

Wakilin Aminiya ya ziyarci Fadar Gwamnatin, inda ya lura cewa akwai kwanciyar hankali a yankin, inda aka girke motocin yaƙi guda uku a kofar shiga gidan gwamnatin.

Wani jami’in tsaro ya tabbatar da cewa an sauya dukkanin jami’an tsaron da ke aiki a Fadar Gwamnatin Jihar.

“Gwamna ya fice daga ciki, kuma muna jiran sabon shugaba ya iso. Komai na tafiya lafiya,” in ji shi.

A halin yanzu, al’ummar Fatakwal na ci gaba da harkokinsu yadda suka saba ba tare da wata matsala ba.

Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas a ranar Talata, sakamakon ikicin siyasa da ya dabaibaye jihar.

Sai dai matakin na Shugaban Ƙasa, ya bar baya da ƙura inda mutane ke tofa albarkacin bakinsu kan lamarin.