✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar Shugaban kasa ta fifita ’yan kasa

Rattaba hannun da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a makon jiya a kan dokar Shugaban kasa ta fifita ’yan kasa a aiki muhimmin mataki ne…

Rattaba hannun da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a makon jiya a kan dokar Shugaban kasa ta fifita ’yan kasa a aiki muhimmin mataki ne da gwamnati ta dauka a kokarinta na bunkasa tattalin arzikin kasa, tare da inganta daukacin al’amuran da ke tattare da shi. Dokar da aka ayyana mai taken, ‘Dokar Shugaban kasa ta biyar don tsarawa da aiwatar da ayyuka, tare da daukaka kimar kwangiloli a Najeriya da kimiyya da injiniyanci da kere-kere.’

A cewar Kakakin Shugaban kasa, Malam Garba Shehu ana sa ran umarnin Shugaban kasar zai kara kaimin amfani da kimiyya da kere-kere da kirkire-kirkire don cimma manufofin bunkasa kasa a daukacin al’amuran da ke tattare da tattalin arziki. Shehu ya ce, “Shugaban kasar, bisa la’akari da karfin ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi, ya yi umarnin cewa daukacin hukumomin da ke daukar ma’aikata (ko samar da mayan aiki) su bayar da fifiko a kan kamfanonin Najeriya da masana’antu wajen bayar da kwangiloli gwargwadon tanadin da dokar bayar da ayyuka ta 2007. Umarnin Shugaban kasa ya kuma haramta wa Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida bayar da izinin shigowa kasar nan ga ma’aikata ’yan kasar waje, wadanda ake da kwararru kwatankwacin irinsu a Najeriya. Sai dai an yi nuni da cewa inda ake kishirwar kwararrun, masu bayar da aikin za su bayar da dama ga kamfanonin kasashen waje da masana’antu wadanda aka tabbatar da kimar tsarinsu na inganta wadanda ake da su a kasa, kafin ma a ba su irin wadannan kwangiloli.”

Duk da cewa daidaikun ’yan Najeriya da kamfanoni a tsawon shekaru sun nuna tabbacinsu na kwarewa da kirkire-kirkire a fannoni da dama, kwazonsu na dakushewa saboda zagon kasan ’yan Najeriya, wadanda suka fi bayar da fiffiko ga kayayyakin kasashen waje da ’yan kwangilarsu. Jami’an gwamnati a kowane mataki suna da wani tunani na cewa kayan (da aka samar ko kera a) kasashen waje da ma’aikata baki ’yan kasar waje a koyaushe sun fi nagarta kan (na) ’yan kasa. Babu wani shiri da ake da shi a kasa da a hankali, a hankali zai rika bayar dama ga masu sarrafa kayayyaki na cikin gida da ’yan kwangila su inganta kwarewarsu. Wannana bin takaici na ci gaba a tsawon shekaru. Wannan matakin abin a yaba ne ganin yadda Shugaban kasar ya yanke matsayar bayar da dama ga masu ayyuka (da samar da kayayyaki) a cikin gida sun inganta kwarewarsu da kayayyakinsu ba tare da yin gasa da kamfanonin kasashen waje ba.

Sannan za a kare ayyukan da ’yan Najeriya ke iya yi, a bude wasu kafofi ga wasu.Tunda kamfanonin kasashen waje sun mamaye masa’antunmu, shi ya sa suke son daukar ma’aikata ’yan kasashen waje ko akwai kwararre dan Najeriya da zai iya yin aikin. Kamata ya yi a samar da matattarar adana bayanai kan kwararrun ’yan Najeriya, ta yadda za a iya nemansu a duk lokacin da bukata ta taso. Bisa la’akari da wannan lamari muna bayar da shawara ga kungiyoyin kwadago da kungiyoyin kwararru su yi amfani da wannan dama wajen bunkasa kwararewarsu ta yadda za su cike wawakeken gibin da ake da shi a cibiyoyin sana’o’in hannu, wadanda suka yi rugu-rugu, suka balbalce ko a mayar da su wajen horar da kananan ma’aikata don su samu kimar da za a amince da su.

Tabbatar da aiwatar da wannan umarni na bukatar kyakkyawan sa-ido ga daukacin sassan gwamnati da ke tabbatar da doka tare da hukumomin tsaro. Hukumar Shigi da Fici ta Najeriya tana da aikin da ya zama dole ta yi wajen ware wani kaso ga ma’aikata ’yan kasar waje a fannin da kawai bukatar hakan ta bayyana karara. Domin tabbatar da umarnin yadda ya kamata dole ne ta bunkasa kwarewarta a wannan fanni, sannan ta katange kanta daga cin hanci da rashawa, musamman daga kamfanonin kasashen waje. Tabbas akwai bukatar kwararrun ma’aikata ’yan kasar waje a manyan kamfanonin sadarwa da masana’antun kere-kere, amma a kayyade yawan kwararrun bakin ma’aikatan da takaita wa’adin aikinsu, tare da kwararran shirye-shiryen tabbatar da cewa ’yan Najeriya sun samu irin wannan kwarewar cikin kankanen lokaci. Ana bukatar cikakken hadin kan kungiyoyin kwararru ta yadda za su taimaka wajen gano ko akwai bukatar wani fanni na kwarewa daga waje.

A wani bangaren, miyagun ’yan kasuwa na iya hada kai da kamfanonin kasashen waje, wajen kumbiya-kumbiya don keta dokar ta hanyar shigo da kayayyakin kasashen waje a matsayin wadanda aka yi a cikin gida. Bisa la’akari da kafofin tsallaka kan iyakokinmu, dole ne a yi kokarin shawo kan yiwuwar kwata irin wannan.

Wannan doka kan abin da ke samarwa a gida  kadai ba za ta cimma daukacin manufa da tasirinta ba, har sai ta samu tagomashi da tallafin wasu matakan da za su bunkasa darajar ilimi da nagartar sana’a’o’in hannu a ma’aikatan Najeriya. Hanya mafi sauri da za a samar da nagartar dabarun aiki bisa kimar ma’aunin duniya ita ce a samu gogewa a wurren ayyuka na kasashen waje, wadanda gwamnati za ta karfafa gwiwar yin hakan bisa hikima. Ire-iren wadannan shirye-shiryen ana bukatarsu domin kara zaburar da masu samar da kayayyaki na cikin gida. Suna bukatar dimbin tallafi da karfafa gwiwa ta yadda za su iya cike gurbin a cikin kasa.