✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dokar hana fita ta koma sa’a 24 a Taraba

Gwamnatin Jihar Taraba ta sanya dokar hana fita ta sa’a 24 a garin Jalingo da Wukari bayan ’yan daba sun wawure kaya a ma’ajiyar kayan…

Gwamnatin Jihar Taraba ta sanya dokar hana fita ta sa’a 24 a garin Jalingo da Wukari bayan ’yan daba sun wawure kaya a ma’ajiyar kayan gwamnati.

’Yan daba sun wawure gidan saurkar baki da Sakatariyar Karamar Hukumar Wukari da Ma’aikatar Gona da dakin ajiyar kayan gwamnati a cikin dare inda suka yi awon gaba da dukiya ta miliyoyin Naira.

Sun kuma mamaye gine-ginen da aka ajiye kayan tallafin COVID-19, takin zamani da sauran dukiyoyin gwamnati a Jalingo da Wukari suka kuma wawushe kayayyakin.

Matasan sun kuma farfasa shaguna da ma’ajiya mallakin daidaikun mutane a Jalingo lamarin da ya tilasta wa gwamnatin jihar tsawaita dokar hana fitar zuwa sa’a 24.

Aminiya ta lura an jibge karin ’yan sanda a Jalingo yayin da aka kafa shingayen bincike a wani bangare na garin.

Sai dai duk da dokar, gidajen mai da kamfanoni da baburan haya sun ci gaba da gudanar da ayyukansu.

%d bloggers like this: