✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar hana fita: Kwalliya na biyan kudin sabulu?

A farkon makon nan ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da tsawaita dokar mako biyu da aka kafa a jihohin Legas da Ogun da ma…

A farkon makon nan ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da tsawaita dokar mako biyu da aka kafa a jihohin Legas da Ogun da ma Yankin Babban Birnin Tarayya a wani jawabi da ya yi ga ’yan kasa ta gidajen rediyo da talabijin.

Ko da yake masana da dama sun goyi bayan matakin na gwamnatin tarayya, wasu ko suka suke yi suna masu cewa a maimakon ta taimaka sai dai ma dokar ta kara dagula al’amura.

Wani abin tambaya dai shi ne: shin kwalliya na biyan kudin sabulu kuwa? Ta biya a mako biyu na farko?

Kwalliya na biyan kudin sabulu?

A jawabinsa, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce dokar ta ba da damar gano sama da kashi 90 cikin 100 na mutanen da ake bibiya ko dai saboda sun dawo daga kasashen waje, ko kuma sun yi mu’amala da wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus.

“Zuwa yanzu mun gano kashi 92 cikin 100 na wadanda suka yi mu’amala da wadanda aka tabbatar sun kamu, yayin da aka ninka dakunan binciken cutar sau biyu; mun kuma kara yawan mutanen da muke yiwa gwaji zuwa mutum 1,500 a kullum”, inji shi.

Da ma dai tun lokacin da aka ayyana dokar ta mako biyu da farko wannan na cikin dalilan da shugaban kasar ya gabatar na rufe yankunan uku.

Da yake karin haske a kan wannan nasara kwana guda bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya ambace ta, Ministan Yada Labarai Lai Mohammed, wanda mamba ne a Kwamitin Cika-Aiki na Shugaban Kasa a Kan Yaki da Coronavirus, wasu alkaluma ya bayar.

A cewarsa, an yi nasarar zakulo mutum kusan 8,932 a fadin Najeriya, wadanda aka sanya su killace kansu na tsawon mako biyu, ko aka yiwa gwaji, ko kuma aka killace don a yi masu magani.

Kwana guda bayan nan kuma Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya ce adadin wadanda aka zakulo ya kai 9,027.

Kalubale

Sai dai kuma da ma tun lokacin da ministan ya ce hukumomi na zabarin mutum sama da 4,000 ya koka da cewa akwai wadanda suka bayar da lambobin waya da adireshi na bogi, wadanda gano inda suke ke da wahala.

Shi ma shugaban kasa ya bayyana cewa wani kalubale da ya taso ya kuma sa dole a tsawaita dokar hana fitar shi ne yadda cutar ta fara yaduwa a tsakanin mutanen da ba su yi tafiye-tafiye zuwa kasashen waje ba kuma ba su yi hulda da wadanda suka fita ba.

Sai dai kuma bayan ayyana dokar a karo na farko, mutane sun yi ta barin yankunan da za ta yi aiki, musamman Abuja da Legas, suna tafiya wasu sassan kasar.

Sai ga shi a daidai lokacin da ake shirin tsawaita dokar ne aka ba da sanarwar samun mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar Kano, aka kuma ce ya yi tafiye-tafiye zuwa Legas da Abuja da Kaduna.

Sannan a jihar Kaduna aka samu wani maigadi, wanda aka ce ya saci jiki ne ya shiga jihar daga Legas. yana dauke da cutar.

Abin da babu tabbas a kai dai shi ne ko mutum nawa ne suka kwashi kwayoyin cutar daga yankunan da aka ayyana dokar zuwa wasu sassan na Najeriya.

Abin da masana suka hango

Wasu masana a Najeriya dai na ganin hana fita da sauran harkoki tsari ne da aka aro daga Turai kuma ba su ma dace da yankuna irin Najeriya ba.

Daya daga cikin masu wannan mahanga shi ne Farfesa Jibrin Ibrahim, wani masanin siyasa, mai fafutukar tabbatar da dimokuradiyya, kuma mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Farfesa Ibrahim ya ce talaka na cikin wani yanayi na gaba kura baya sayaki.

“Kamar yadda muka sani, talakawa na da zabi biyu game da manufar nisanatar juna: ko su zauna a gida yunwa ta kashe su, ko kuma su fita watakila COVID-19…[ta] kashe su”, sannan ya yi wata tambaya: “Shin ba zai yiwu mu samar da wata manufa da ta fi dacewa da yanayinmu ba ne?”

Da yake bayyana irin wannan ra’ayi a wata makala da ya rubuta a jaridar Daily Trust ta ranar Alhamis, shugaban kamfanin Urban Shelter, Alhaji Ibrahim Aliyu, shawara ya bayar cewa a maimakon a aro abin da ake yi a galibin Turai, da wadanda suka fi shiga hadarin kamuwa da cutar, kamar tsofaffi da marasa lafiya, aka killace aka ba su tallafi.

Duk da haka…

Amma fa wasu masanan na ganin gara da aka yi wannan doka.

Ko da yake yana ganin gwamnatin Najeriya ba ta da kyakkyawan tsarin da zai ba ta damar yaki da cutar coronavirus, tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, ya goyi bayan wannan mataki.

A cewarsa, “Gaskiya dole a goyi bayan gwamnati a kan wannan sha’ani domin babu zabi kuma akwai hatsari idan ba a goyi bayan gwamnati ba”.

Dokta Laz Ude Eze, wani masanin harkar lafiyar al’umma ne, kuma jagoran wata kungiyar farar hula mai fafutukar ganin a inganta asibitoci mai suna Make Our Hospitals Work Campaign.

Shi ma a ganin shi, matakin tsawaita dokar ya dace saboda a cikata ladan da aka samu a zangon farko.

“Wannan ce hanya mafi inganci ta hana cutar coronavirus yaduwa”, inji masanin.

Game da tsananin da talakawa za su shiga kuwa, cewa ya yi: “Saboda haka ina kira ga gwamnatoci da su tabbatar cewa abubuwan tallafi da suke warewa ya kai ga hannun wadanda suka yi abin domin su”.

An dai ce ba a san maci tuwo ba, sai miya ta kare; mai yiwuwa ba za a san cikakken tasirin da dokar ta yi ba sai bayan wadannan makwanni biyu.