✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Dole ce ta sa mu tsawaita dokar hana fita —Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce dole ce ta sa a tsawaita dokar hana fita kwatakwata a Yankin Babban Birnin Tarayya da jihohin Legas da Ogun…

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce dole ce ta sa a tsawaita dokar hana fita kwatakwata a Yankin Babban Birnin Tarayya da jihohin Legas da Ogun da makwanni biyu.

A wani jawabi da ya yi ga al’ummar kasa ta gidajen rediyo da talabijin da maraicen Litinin, Shugaba Buhari ya ce hana zirga-zirga da nesanta tsakanin mutane da kuma hana tarukan jama’a ne kadai hanyoyin dakile annobar coronavirus.

“…[B]ayan na duba rahotannin Kwamitin Cika-Aiki na Shugaban Kasa a Kan Yaki da Coronavirus da kuma zabin da muke da shi da idon basira, ya zama wajibi a tsawaita dokar hana fita a jihohin Legas da Ogun da ma Yankin Babban Birnin Tarayya da karin kwana 14 tun daga karfe 11.59 na daren Litinin 13 ga watan Afrilu…”

Shugaban ya kara da cewa, “Wannan ba abin wasa ba ne, lamari ne na rayuwa ko mutuwa”, kuma tun da an rufe cibiyoyin manyan addinai na duniya, wasu kasashen duniya ma sun hana fita kwatakwata, “ba zai yiwu mu yi sakaci ba”.

Nasarorin da aka yi

Shugaban ya fadi haka ne dai bayan ya bayyana irin ci gaban da ya ce an samu a makwanni biyun da aka yi a baya na hana fitar.

“Zuwa yanzu mun gano kashi 92 cikin 100 na wadanda suka yi mu’amala da wadanda aka tabbatar sun kamu, yayin da aka ninka dakunan binciken cutar sau biyu; mun kuma kara yawan mutanen da muke yiwa gwaji zuwa mutum 1.500 a kullum.

“Mun kuma horar da ma’aikatan lafiya 7,000 a kan dabarun dakile cututtuka masu yaduwa yayin da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta tura ma’aikatanta zuwa jihohi 19.

“Zuwa yau Legas da Abuja na da wuraren da za a iya killace majinyata 1,000 ko wacce…”

Sai dai kuma, a cewar Shugaba Buhari, akwai matsala.

Amma akwai matsaloli

“Na damu matuka da yadda ake samun karuwar wadanda suka kamu da cutar da wadanda suka rasa rayukansu a fadin duniya da Najeriya musamman….

“A nan Najeriya a ranar 30 ga watan Maris muna da wadanda aka tabbatar sun kamu mutum 131 da wadanda suka mutu su biyu a jihohi 12.

“Da safiyar yau [Litinin], an samu mutum 323 da aka tabbatar sun kamu a Najeriya a jihohi 20. Abin takaici mutum 10 sun rasu…”

Wata matsalar da shugaban kasar ya bayyana kuma ita ce ta yanayin kamuwa da cutar ta COVID-19.

“Hukumar NCDC ta shaida min cewa da dama daga cikin sabbin kamuwar a tsakanin al’umma ne [ba wadanda suka yi mu’amala da wadanda suka shigo da ita daga kasashen waje ba], daga mutum guda zuwa wani. Don haka dole ne mu mayar da hankali ga hadarin cudanya ta kut-da-kut a tsakanin mutane”.

Karin wata matsalar da Shugaba Buhari ya ce abin dubawa ce kuma ita ce ta tsananin da wannan mataki ka iya jefa al’umma a ciki, yana mai cewa babu wata kasa da tattalin arzikinta zai jure rashin zirga-zirgar jama’a.

“Ina sane da cewa wasunku sai sun fita suke samun abin da za su ci, kamar ‘yan tireda da leburori da masu aikin hannu.

“Rayuwar wadannan mutane ta dogara ne a kan fitarsu da cudanyarsu da wasu…, Amma duk da haka ba za mu sauya dokar ba”.

Tallafi ga talakawa

Sai dai shugaban kasar ya ce za a ci gaba da bayar da tallafin da aka sanar za a bayar makwanni biyu da suka wuce, wadanda suka hada da raba abinci da kudi ga marasa galihu da kuma jingine kudin ruwan da ake dora wa wadanda suka karbi bashin bankuna.

Ko da yake mutane da dama na ta korafin cewa ko dai tallafin bai kai gare su ba, ko kuma abin da aka ba su bai taka kara ya karya ba, shugaban kasar dai ya ce za a kara a kan haka.

“Na kuma bayar da umarnin a kara yawan iyalan da aka yiwa rajista a kundin mutanen da suka fi kowa talauci daga miliyan 2.6 zuwa miliyan 3.6 a makwanni biyu masu zuwa”.

Shugaban ya kuma ce ya umarci wasu ministocinsa su yi aiki da Kwamitin Cika-Aiki a Kan Coronavirus don bullo da manufofin kare tattalin arzikin Najeriya daga illar COVID-19 da kuma tabbatar da cewa cutar ba ta yi kafar ungulu ga aikin gona ba.