✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar hana fita: Abu uku da suka yi wa matan Kano dadi

Kusan mako guda ke nan tun bayan fara aiki da dokar hana zirga zirga da gwamnatin jihar Kano ta kafa. Yayin da maza ke kokawa…

Kusan mako guda ke nan tun bayan fara aiki da dokar hana zirga zirga da gwamnatin jihar Kano ta kafa.

Yayin da maza ke kokawa da yadda dokar “ta takura musu”, su kuwa  wasu matan jihar cewa suka yi abin ya yi musu dadi.

Ga uku daga cikin dalilansu:

  1. Komai ya wadata

Wasu mazan ba su cika son su yo cefane na dogon lokaci ba, sai dai kullum su bayar da na sayen abin da ake bukata a ranar.

Amma saboda wannan doka magidanta da dama sun sayo isassun kayan abinci da sauran kayan bukatu na yau da kullum sun ajiye.

Hakan ya yi wa Malama Asabe Audu dadi sosai.

“Kin ga a jajiberin ranar da dokar za ta fara aiki sai da maigidan nan ya shigo da kusan komai da muke bukata ba kamar a da ba da yake bari na da cikon kudin cefane, domin kudin cefanen da yake ba mu ba sa isa”, inji ta.

  1. Lokacin iyali ya karu

Wasu magidantan kan yi sammakon fita, musamman ma’aikata.

Idan an dawo da yamma kuma za a fita majalisa ko a kada wani wurin; in ba sa’a ba sai lokacin barci za a gan su.

Amma saboda wannan doka akalla maigida yana samun lokacin kasancewa tare da iyalinsa.

Wannan ne ya yi wa mata irin su Barira Jatau dadi.

“Kasancewar maigidana ma’aikacin banki ne ya sa sai kawai a ranakun karshen mako muke kasancewa tare [amma yanzu lamarin ya sauya].

“A gaskiya duk da cewa ba son zaman kullen ake yi ba, amma mun ji dadin hakan”, inji Barira.

  1. ‘Me ya fi rai na?’

Su ma matan a bangarensu dokar ta tilasta wa wasu yin abubuwan da a da ba su da lokacin yi.

Hakan kuma ya sa daga su har abokan zamansu, kowa ke jin dadin wannan doka.

Alal misali, Malama Salamatu Danja ma’aikaciyar gwamnati ce wacce a da ba ta da lokacin girki saboda tana fita aiki.

Amma saboda wannan doka ta samu cikakken lokacin zama a gidanta ba kamar a baya ba.

“A yanzu kin ga ina zama in shiga kicin na yi girki sosai ba kamar a baya ba da nake fita aiki; [a lokacin] sai dai na dafa dafadukan taliya ko makaroni saboda a ko yaushe a makare nake fita haka kuma a makaren nake dawowa.

“Shi ma maigidana da yara sai murna suke yi da zaman da muke tare. Hakan ya sa muna kara fahimtar juna”, sannan kuma ya sa Malama Salamatu ta ji dadin dokar.

Naman wani, gubar wani

Sai dai kuma ba a taru an zama daya ba.

Sakamakon wannan doka ta zaman gida wasu matan, kamar Hajiya Indo ‘Yankura, ba sa jin dadi.

“A gaskiya zaman nesa da juna ya fi dadi musamman idan ya kasance maigidan ba shi da kudi domin sai dai a yi hakuri kawai”.

 

Saboda wasu dalilai mun sakaya sunayen matan da muka zanta da su wajen hada wannan rahoton. Don haka ba sunayen matan na asali muka ambata ba.