✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dokar Cire Kudi: Emefiele Ya Wuce Gona Da Iri —Dan Majalisa

Dan Majalisar Tarayya na zargin CBN da neman shiga aikin Hukumar EFCC

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya wuce makadi da rawa a sabuwar dokar kayyade kudaden da ’yan Najeriya za su iya cirewa daga asusun bankinsu, in ji wani dan Majalisar Tarayya.

Honorabul Mark Gbillah daga Jihar Binuwai, ya ce dokar takaita cire kudade da bankin CBN ya bullo da shi yin katsalandan ne a aikin Hukumar EFCC, mai yaki da masu karya tattalin arziki.

Dan Majalisar ya bayyana haka ne hirar da aka yi da shi a tashar talabijin ta Channels kan sabuwar dokar, wadda ta yamutsa hazo.

Yadda CBN ya kayyade cire kudi

Sabuwar dokar ta kayyade cire tsabar kudi daga asusun bankin mutane zuwa N20,000 ta cibiyoyin cire kudi na POS da kuma N100,000 daga kan kanta a cikin banki.

Kamfanoni kuma an kayyade musu cire N100,000 ta POS da kuma 500,000 a cikin banki.

Sakon da CBN ya aike wa bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade, ya bayyana cewa N100,000 ne iya tsabar kudin da mutum zai iya cirewa ta POS a mako, ko kuma N500,000 a cikin banki.

Kamfanoni kuma abin da za su cira ta POS a mako shi ne N500,000, ko kuma miliyan 10 a cikin banki.

Masu son cire fiye da kudaden da aka kayyade kuma, CBN ya shardanta musu cike wasu takardu da kuma biyan kaso 10 cikin dari na yawan kudin da za su cira a matsayin caji; daidaikun mutane kuma canjin kashi biyar cikin dari.

Majalisa ta gayyaci Gwamnan CBN

Tuni dai zaurukan Majalisar Dokoki ta Kasa ta bukaci Emefiele ya bayyana a gabanta a makon gobe, don amsa tambayoyi kan sabon tsarin wanda Majalisar ta soka, da cewa zai jefa ’yan kasa musamman kananan ’yan kasuwa cikin kangi.

Babu gudu ba jand baya —Emefiele

Amma jim kadan bayan zaman Majalisar na ranar Alhamis, Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya ce babu gudu babu ja da baya a kan sabon tsarin.

Ya bayyana cewa manufar tsarin shi ne bunkasa tsarin Hada-hadar kudade da hanyoyin zamani da kuma takaita zirga-zirgar tsabar kudi.

A baya-bayan nan dai CBN ta yi kaurin suna a wurin ’yan Najeriya tun bayan da ya sanar da bullo da sabbin takardun N200, N500 da kuma N1,000 da za a fara amfani da su ranar 15 ga watan Disamba da muke ciki.

A yayin karin bayani, Emefiele ya ce lokacin sauya takardun kudin da doka ta tanadar ya dade da yi, sannan magance matsalar buga jabun takardun kudin.

Emifiele, wanda ya ce bayan fitowar sabbin takardun kudin, za a daina sanya takardun Naira 1,000 a injina cire kudi (ATM) ya ce sauya takardun kudi zai tilasta wa wadanda suka taskance tsabar kudi a gidajensu su fito da su zuwa bankuna, sannan ya karya tattalin arzikin ’yan ta’adda da ke karbar makudan kudade a matsayin fansar mutanen da suka yi garkuwa da su.

Gwamnan CBN ya kwafsa —Masani

Amma da yake tsokaci kan sauya takardun kudin, Farfesa Frank Ozor na Sashen Nazarin Tattalin Arziki a Jami’ar Tarayya ta Nduffu, ya ce, CBN ta yi wauta kan batun sauya takardun kudin.

A cewarsa, “Wannan tsari bai dace ba, idan aka yi la’akari da yanayin rayuwar al’ummar kasar nan.

“CBN ba ta yi bincike ta gano adadin tsabar kudin da zai wadatar da jama’a, musamman a yankunan karkara wajen biyan muhimman bukatunsu ba.

“Wannan dai za a iya cewa ya yi shirme wajen buga sabbin takardun kudaden,” in ji masanin tattalin arzikin.