✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dogo Giɗe ya kashe ’yan Boko Haram 20 ya ƙwace makamansu

Dogo Giɗe ya fitar yana bugun ƙirji da ɓarnar da ya yi wa Boko Haram, ya kuma yi baje kolin makamansu da ya ƙwace

Ƙasurgumin ɗan bindiga Dogo Giɗe ya kashe mayaƙan Boko Haram 20 a wata arangama da aka yi tsakanin ’yan ta’addan a tsakanin Jihar Neja da Zamfara.

Rahotanni sun nuna mayaƙan Boko Haram daga ɓangaren Sadiƙu ne suka yi wa Dogo Giɗe kwanton ɓauna da nufin kashe shi, inda a yayin ƙazamin faɗan Dogo Giɗe ya kashe mayaƙan Boko Haram 20 tare da ƙwace manyan makamansu.

Ƙazamin faɗan, kamar yadda rahotanni suka nuna ya auku ne a yankin Dajin Kwantannkoro da ke tsakanin jihohin Neja da Zamfara.

A wani bidiyo da ɗan ta’adda Dogo Giɗe ya fitar yana bugun ƙirji da ɓarnar da ya yi wa Boko Haram, ya kuma yi baje kolin makamansu da ya ƙwace da suka hada da bindigogi 10 ƙirar AK47 da makaman roka da wayoyin hannu da katinan shaida.

A cikin bidiyon, Dogo Giɗe ya ce, “Sadiku da ƙungiyarsa sun kawo mana harin kwanton ɓauna, amma mun yi nasara, mutuminmu ɗaya kawai ya samu rauni, amma mun kashe musu kusan mutum 20,” yana mai sukar ɓangaren Sadiku da kai wa fararen hula hari da sunan jihadi.

Gabar Boko Haram da Dogo Giɗe ya buɗe wani sabon babi a yanayin ayyukan ’yan ta’adda da masu tsattsauran ra’ayi a yankin, inda ɗaukar fansa a tsakaninsu ke tasiri a rikicin nasu.

Rikicin ’yan bindiga da Boko Haram

Rahotanni sun nuna cewa gabar tasu ta samo asali ne daga kisan ɗan uwan Dogo Giɗe da Boko Haram ta yi a shekarar 2023, lamarin da ya sa Giɗe ya katse alaƙa da ƙungiyar tare da alwashin ɗaukar fansa.

Tun daga lokacin yake ta ƙoƙarin kawar da Boko Haram daga yankunan da yake da ƙarfi musamman a Ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja, inda ya kawar da shingayen da mayaƙan ƙungiyar ta kafa.

Wakilinmu ya ruwaito cewa a baya-bayan nan an ji Dogo Giɗe na kira ga mazauna yankin da suka yi ƙaura cewa su dawo garuruwansu, inda ya yi alƙawarin daidaita al’amura tare da neman tafiyarsu.

Faɗan ƙungiyoyin ’yan bindiga

A shekarar 2024 an kashe aƙalla shugabannin ’yan bindiga biyar da kuma mayaƙansu a rikicin ƙungiyoyin ’yan bindiga da ya ɓarke a Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Daga cikin shugabannin ’yan bindigar da aka kashe har da Dogo Bali da Ɗan Makaranta da Malam Gainaga da Mallam Tukur da Malam Jaddi.

Rikicin ya ɓarke ne tsakanin ƙasurgumin jagoran ’yan bindiga, Ado Aliero a ɓangare guda, da kuma ɓangarorin Kachalla da Dogo Bali, da suka yi masa taron dangi.

Faɗan ya ɓarke ne bayan Kachalla ya yi watsi da gargaɗin da Ado Aleiro ya yi masa cewa ya daina kai hare-hare kan ƙauyukan da ke yankin ’Yankuzo da kewaye — wanda Aliero ke iƙirarin yana ƙarƙashinsa ikonsa.

Faɗan ya auku ne a ƙauyukan ’Yankuzo da ’Yan Waren Daji da Munhaye da Mada in Tsafe Ƙaramar Hukumar Tsafe.

Ana zargin Kachalla ya gayyato abokinsa Dogo Bali domin kai hari a ’Yankuzo, inda a yayin da suke can ne Aliero da yaransa suka yi musu kwanton ɓauna suka da kashe da dama daga cikinsu, suka kuma jikkata wasu da dama.

Aminiya ta gano cewa a yayin musayar wutar ta kusan awa bakwai ɓangaren Aliero ya kashe huɗu daga cikin manyan jagororin ’yan bindiga: Dogo Bali da Ɗan Makaranta da Malam Gainaga da Mallam Tukur da kuma Malam Jaddi.

Aleiro ya kuma kai hari kan sansanin fitaccen jagoran ’yan bindiga Alhaji Ɗan Najeriya a yankin ’Yan Waren Daji, wanda shi da yaransa suka tsere suka bar makamansu, bindigogi ƙirar AK47 guda 170, kamar yadda muka samu bayani.

Bayan ɓullar labarin kashe Bali, faɗan ya faɗaɗa zuwa sansanonin wasu shugabannin ’yan bindiga da ke alaƙa da shugabannin ’yan bindigar uku, a ƙauyukan Mada da Munhaye da kuma ’Yanwaren Daji.

An kashe ’yan bindiga da daman gaske a yayin musayar wutar tsakanin ɓangarori uku a Dabar Gahori, ɗaya daga cikin manyan sansanonin ’yan bindiga daga ɓangarori daban-daban a Jihar Zamfara.