Gwamnatin Jihar Nasarawa ta raba kekunan dinki ga ’yan gudun hijira 166 a jihar da aka yaye bayan an kammala ba su horo a kan sana’ar dinki.
Gidauniyar UNDP tare da hadin gwiwar Gwamnatin Kasar Japan ne suka dauki nauyi shirin horaswar.
- Kwalara ta kashe mutum 11, ta kwantar da 200 a Taraba
- Batanci ga Annabi: Deborah ta wuce gona da iri —Farfesa Maqari
Baya ga kayan aiki da aka raba wa wadanda suka samu horon, an kuma mika wa kowannensu takardar shaidar kammala koyon sana’ar diniki.
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa, tare da wakilan UNDP da Gwamnatin Japan me suka jagoranci mika kayayyakin ga wadanda aka bai wa horon, a wurin taron raba kekunan a gidan gwamnatin jihar, da ke Lafia a ranar Juma’a.
Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin sun bayyana farin cikinsu dangane da tallafin da suka samu, tare da ba da tabbacin cewa za su yi bakin kokarinsu wajen yin amfani da kayan don cin ma manufarsu.