✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dogara ga Ubangiji 1

Muna yi wa Ubangiji Allah godiya domin kaunarSa da alherianSa zuwa gare mu. Barkanmu da sake saduwa a wannan mako.  Da yardar Ubangiji za mu…

Muna yi wa Ubangiji Allah godiya domin kaunarSa da alherianSa zuwa gare mu. Barkanmu da sake saduwa a wannan mako. 

Da yardar Ubangiji za mu yi nazari ne a kan dogara ga Ubangiji. Mun sha jin wannan batu, amma Ubangiji Yana son mu yi koyi da wani abu a cikin sakonSa. Bari Allah Ya ba mu ganewa, amin.

Za mu fara da karatu cikin Littafin Karin Magana 3:5-7: “Ka dogara ga Ubangiji da zuciya daya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani. A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, Shi kuma zai nuna maka hanyar da take daidai. Sam, kada ka yarda ka dauki kanka kai mai hikima ne fiye da yadda kake, kai dai ka ji tsoron Ubangiji, ka rabu da aikata mugunta.”

Muna rayuwa ne cikin zamanin da dogara ga ilimi da dukiya da iko da matsayi ko karfin halin mutum ya cika zukatan mutane. Mutane da dama ba su da tsoro da kuma sanin Allah cikin zukatansu, sun fi dogara da dukiya da matsayi da kuma iliminsu, suna ganin cewa wadannan abubuwa da suka mallaka za su fisshe su. Ta wani bangaren kuma tallauci da rashin lafiya da matsalolin rayuwa na yau da kullum sun bi sun mamaye tunanin mutane har ta kai ga mantawa da cewa akwai Allah. Ta dalilin haka ne za ka ga wadansu suna shiga halayen da ba su kamata ba. Misali yin maye da kwace ko fashi da makami da zamba da damfara da garkuwa da mutane da makamantansu har takan kai ga kisan kai. Haka yakan faru ne idan mutum ya dogara ga ikon kansa. A ganinsa, yin irin wadannan abubuwa ko zama cikin wannan hali zai biya masa bukata, amma ina, idan muka lura, mutum ba ya taba cin nasara cikin rayuwarsa idan bai dogara ga Ubangiji ba.

A cikin karatunmu na farko mun ga cewa: “Ka dogara ga Ubangiji da zuciya daya kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani…” Ga wadansu, wannan batu almara ce kawai ba gaskiya a cikinta, amma idan za mu yi tunani, wai shin mutum yakan iya kara wa kansa sakan daya ne don ya rayu, ko mu ce zai iya sayen rabin sakan da dimbin dukiyar da yake da ita a nan duniya? Bari mu ga abin da Yesu Almasihu ya fada a cikin Littafin Matiyu 6:26-34: “Ku dubi dai tsuntsaye. Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba sa kuma tarawa a rumbuna, amma kuwa Ubanku na sama Yana ci da su. Ashe, ko ba ku fi martaba nesa ba? Wane ne a cikinku, don damuwarsa, zai iya kara ko da taki ga tsawon rayuwarsa? To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi dai furannin daji, yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baki, duk da haka ina gaya muku, ko Sulaimanu ma, shi da adonsa duk, bai taba yin adon da ya fi na dayansu ba. To, ga shi, Allah Yana kawata tsirran daji ma haka, wadanda yau suke raye, gobe kuwa a jefa su a wuta, balle ku? Ya ku masu karancin ban-gaskiya! Don haka kada ku damu, cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ ko kuwa, ‘Me za mu sa?’ Ai, al’ummomi ma suna ta neman duk irin wadannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa Ya san kuna bukatarsu duka. Muhimmin abu na farko, sai ku kwallafa rai ga al’amuran mulkin Allah da kuma adalcinSa, har ma za a kara muku dukan wadannan abubuwa. Saboda haka kada ku damu don gobe, ai, gobe ta Allah ce. dawainiyar yau ma ta ishi wahala.”

Ga mai damuwa, dogara ga Ubangiji ita ce mafita, idan kuma kana alfahari da dukiyarka ne, ka ji abin da Yesu Almasihu ya fada, “…Ku dubi dai furannin daji, yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baki, duk da haka ina gaya muku, ko Sulaimanu ma, shi da adonsa duk, bai taba yin adon da ya fi na dayansu ba.”  Illiminka da matsayinka da dukiyarka, ba ka fi furan daji ba, to me ya sa a zamanka na mutum ba za ka yi tunanin cewa abubuwan da ka mallaka duk banza ne, idan ba ka dogara ga Ubangiji Allah ba.

Wadansu suna ganin cewa ai idan kana da mukami da dukiya za ka iya gina ganuwar rudunar masu tsaro kewaye da kai domin kada wani abu ya same ka. Saurari abin da Zabura 118: 8-9 ke fadi: “Gwamma a dogara ga Ubangiji da a dogara ga mutane. Gwamma a dogara ga Ubangiji da a dogara ga shugabanni na mutane kawai. Dalili kuwa shi ne Ubangiji Allah Shi ne Mahaliccinka, Yana da iko Ya kare ka Ya kuma dauke ranka, Shi ne Mai azurtawa Mai kuma biyan bukata, ba Ya gyangyadi ko ya yi barci, ba Ya kuma gajiya, Yana cike da jinkai da girma da iko bisa kowane abu a sama da kasa, idan har ba ka san wannan ba, kai ji abin da Ubangiji ke fadi a cikin Littafin Irimiya 17:5-8, Ubangiji Ya ce: “La’ananne ne mutumin da ke dogara ga mutum, Wanda jiki ne makaminsa, Wanda ya juya wa Ubangiji baya, gama yana kama da sagagi a hamada, Ba zai ga wani abu mai kyau yana zuwa ba. Zai zauna a busassun wuraren hamada, A kasar gishiri, inda ba kowa. “Mai albarka ne mutumin da ke dogara ga Ubangiji, Wanda Ubangiji ne madogararsa. Shi kamar itace ne wanda aka dasa a bakin rafi, Wanda ke mika saiwoyinsa zuwa cikin rafin, Ba zai ji tsoron rani ba, Kullum ganyensa kore ne, Ba zai damu a lokacin fari ba, Ba zai ko fasa yin ’ya’ya ba.”

Za mu ci gaba mako mai zuwa da yardar Ubangiji. Shalom.