Ameerah, diya ga malamar Kwalejin Fasaha ta Kaduna (Kaduna Polytechnic) da aka sace, Dokta Ramatu Abarshi, ta kubuta bayan shafe kwana 38 a hannun wadanda suka yi garkuwa da ita.
Wata majiya ta shaida cewar, wanda suka sace ta sun sake ta a ranar Talata, wanda kuma tuni aka garzaya da ita wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba.
- Jesse Lingard ya raba gari da Manchester United
- Yadda 2023 ta tantance Okorocha bayan ya biya kotu belin N500m
Aminiya ta ruwaito cewa an sace Dokta Abarshi da diyarta da kuma direbansu, Ibrahim a ranar 24 ga Afrilun 2022, a kan babbar hanyar Kachiya zuwa Kaduna, a lokacin da suke dawowa daga aikin agaji.
’Yan bindigar sun saki malamar sati uku da ya gabata, yayin da kuma suka saki direban satin da ya wuce, sannan suka saki diyar a ranar Talata.
“Eh, an sako Ameerah ranar Talata da yamma; ta sake haduwa da ‘yan uwanta kafin a kaita wani asibiti da ba a bayyana ba saboda dalilan tsaro. Ba abu ne mai sauki ba amma mun gode wa Allah da ta dawo gida lafiya,” inji shi.
Sai dai majiyar ta shaida wa Aminiya cewar masu garkuwar sun karbi miliyoyin kudi kafin su sake ta.