Kungiyar Direbobin Man Fetur (PTD) ta yi barazanar ficewa daga uwar Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (NUPENG), idan shugabanta Williamsiu Akporeha da sakatare, Afolabi Olawale ba su ajiye mukaman su.
Daya daga cikin shugabannin kungiyar direbobin reshen Ibadan, Gbenga Olawale, ya ce mambobin su za su fara zanga-zanga a fadin kasar nan domin ganin shugabannin na NUPENG sun gaggauta sauka.
Daga nan ya ce sun bukaci duka mambobin su da su sanya ganye a gaban motocinsu a matsayin alamar nuna barin rai.
Olawale ya yi zargin cewa tunda farko Williams ba mamban kungiyar NUPENG ba ne, cuso musu shi aka yi, don haka bai dace ya ci gaba da jagorantar kungiyar ba.
- Hukuncin Zaben Kano: Masu shirin zanga-zanga su shiga taitayinsu —’Yan sanda
- Kano: ’Yan APC sun fara azumi bayan Abba ya garzaya Kotun Koli
“Williams ya sa ’yan koronsa suna karbar kudin haraji daga mambobinmu, kuma ba a yi amfani da shi wajen ci gaban kungiya ko na birebobi ba’, inji Olawale.
A saboda haka, Olawale ya yi kira da a gaggauta shirya sabon zabe, kuma kungiyar PTD ta cimmar nuna goyon bayan ga Lucky Osusan da Dayyabu Garga, a matsayin wadanda suke so su zama sabbin shugabanni NUPENG.