Kungiyar Ma’aikatan Man Fetir da Iskar Gas ta Kasa (NUPENG) ta bayyana damuwa kan yajin aikin malaman jami’o’i ke ci gaba da yi, inda ta yi barazanar goya musu baya.
Ma’aikatan kungiyar sun kuma yi Allah Wadai da halin ko-in-kula da Gwamnatin Tarayya ke nuna wa a kawo karshen yajin aikin.
- 2023: Me ya sa sanatocin APC ke ficewa zuwa wasu jam’iyyun?
- An gano gawar mutum 15 da suka mutu a hatsarin jirgin ruwan Legas
Shugaban Kungiyar na kasa, Kwamared Williams Akporeha da babban Sakatarenta, Kwamared Afolabi Olawale sun ce kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU), da ta wadanda ba malamai ba (NASU) da kuma ta Manyan Ma’aikatan Jami’o’in (SSANU) sun rufe makarantu tsawon watanni, wanda hakan ya dakatar da karatun daliban da kawo zaman banza a tsakaninsu.
Kungiyar ta ce ce idan har gwamnatin ba ta yi maza ta kawo karshen yajin aikin da aka kwashe watanni hudu ana yi ba, to ba ta da zabin da ya wuce fitowa zanga-zanga ta bai daya.
Kungiyar ta kuma ce abin takaici ne yadda a maimakon gwamnatin ta mayar da hankali wajen share wa kungiyoyin hawayensu, sai ta biye wa sauran ‘yan siyasa wajen mayar da hanakalinta kacokan kan yakin neman zaben 2023.
Cikin wata sanarwa da kungiyar ta NUPENG ta raba wa manema labarai, ta ce ta bi sahun sauran takwarorinta wajen nuna rashin jin dadinta kan yadda Gwamnatin Tarayya take tafiyar da lamarin.
“Muna cikin tsananin damuwa kan yadda yajin aiki ya mayar da dubban dalibai zaman ‘yan kashe wando, wasu kuma suka fada aikata miyagun laifuka, ba haka ya dace ya kasance ba, domin kamata ya yi su zamo abin alfaharinmu”, a cewar kungiyar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Wannan abin bakin ciki ne, domin yana haska yadda shugabanninmu na siyasa suka lalata harkar gwamnati da kuma nuna rashin tausayi da ciyar da bangaren ingantaccen ilimin kasar gaba”.
“Don haka kungiyarmu za ta hadu da ta kwadago ta fito zanga-zangar gama gari kan lamarin, kuma muna kira ga ‘yan kungiyarmu da su kasance cikin shirin jiran umarnin kungiyar kwadagon domin fita zanga-zangar da ma yajin aikin”.