✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kano: ’Yan APC sun fara azumi bayan Abba ya garzaya Kotun Koli

Abdullahi Abbas ya bukaci magoya bayan jam'iyyar da ’yan kasuwa su dage da addu'a.

Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta bukaci daukacin mambobinta da ’yan kasuwar da suka yi asarar dukiyarsu sakamakon rushe musu shaguna da gidaje da gwamnatin jihar ta yi da su fara azumi a yau.

Shugaban jam’iyyar, Abdullahi Abbas, a cikin wani sakon murya ya bukaci da su yi addu’a tukuru domin nuna godiya ga nasarar da jam’iyyarsu ta samu nasara a kotun daukaka kara a ranar Juma’a.

Sakon nasa na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP, ya yanke hukuncin kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara a gaban kotun koli.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaransa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, gwamnan ya ce ya umarci lauyoyinsa da su daukaka kara kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke.

Ya kara da cewa yana da kwarin gwiwar cewa “Kotun Koli za ta sauke hukuncin da yardar Allah.”

Tun da fari kotun sauraron kararrakin zabe ta fara soke Abba, hukuncin da kotun daukaka kara ta tabbatar daga bisani.

Hukunci biyu sun haifar da zazzafar muhawara musamman a tsakanin masu sharhi kan al’amuran siyasa a jihar.

Kazalika, hukuncin ya haifar da cece-kuce da fargaba a tsakanin mazauna jihar.

%d bloggers like this: