Kungiyar Direbobin Mai da Iskar Gas ta Kasa (NUPENG) ta direbobin tankokin mai za su fara yajin aiki daga safiyar Litinin a jihar Legas.
Shugaban kungiyar ta NUPENG shiyyar Kudu maso Yamma Tayo Aboyeji ya ce kungiyar rashin cimma matsaya a tattaunawarsu da gwamnatin jihar a ranar Lahadi ya tilasta su shiga yajin aikin .
Ya ce, “Sai dai kawai muka ce za mu tsunduma yajin aiki sannan suka nuna za su saurari bukatunmu da suka hada da cin zarafi da karbar kudade da jami’an tsaro ke yi na ba gaira ba dalili.
“Saboda haka tunda ba su shirya magance wadannan matsalolin ba, mun yanke shawarar tsunduma yajin aiki daga safiyar Litinin har sai an yi abun da ya kamata.
“Abun takaici ne yadda yajin aikin zai shafi dukkan sauran jihohin Najeriya kasancewar yawancinsu daga nan suke dakon man fetur.
“Ba wai murna muke cewa za mu tsayar da komai cik ba, amma ba zai yuwu mu ci gaba da zuba ido wadannan tarin matsalolin na faruwa ba”, inji shi.
Idan za a iya tunawa, a ranar Juma’a shugaban kungiyar NUPENG na kasa, Williams Akporeha ya umarci direbobin tankokin man da su dakatar da aiki daga 12 na daren ranar Litinin har sai gwamanti ta biya musu bukatunsu.