✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Direbobi sun saki hanyar Zariya-Kano bayan sun rufe ta tsawon kwana 3

Tun ranar Laraba dai direbobin suka rufe hanyar saboda kashe musu dan uwa

Bayana shafe kimanin sa’o’i 48 a rufe, daga karshe direbobin tanka sun amince sun saki hanyar Zariya zuwa Kano don nuna tirjiya kan kisan dayansu da suke zargin wani soja da aikatawa.

Aminiya ta gano cewa a ranar Asabar, direbobin dai daga karshe sun amince su janye motocin nasu da suka kange hanyar mai yawan ababen hawan bayan jerin tattaunawa da jami’an tsaro da kuma jami’an Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC).

Aminiya ta rawaio muku yadda direbobin suke toshe hanyar tun misalin karfe 3:30 na yammacin Laraba a kusa da garin Tasahar Yari da ke Karamar Hukumar Makarfi a Jihar ta Kaduna.

Sun dai zargin wani soja da ke aiki da wani kamfanin gine-gine ne ya kashe direban bayan wata sa’insa da ta gifta a tsakanin su.

Lamarin dai ya haifar da cunkoson ababen hawa tsawon wadannan kwanakin, inda ala tilas mutane suka koma amfani da wasu hanyoyin, wasu kuma da dama suka yi curko-curko.

Sai dai da yake tabbatar da labarin da sanyin safiyar Asabar, mai rikon mukamin Kwamandan FRSC na Jihar Kaduna, Lawal Garba, ya ce yanzu lamura sun daidaita a hanyar.

Ya ce, “Ina farin cikin sanar da kai cewa yau [Asabar] a safe, an bude babbar hanyar Zariya zuwa Kano wajen misalin karfe 9:30 bayan shafe kwanaki a kulle.

“Yanzu haka ababen hawa na kaiwa da komowa kamar yadda aka saba, kuma jami’anmu na can sua kokarin tabbatar da komai ya tafi yadda ya kamata,” in ji shi.

Ya ce tun farkon faruwar lamarin sun kasa rintsawa a kokarinsu na ganin an lalubo bakin zaren.

Ya kuma ce ba a sami wata asarar rai ko ta dukiya ba a sakamakon cunkoson.

Idan za a iya tunawa, tuni Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta sanar da kaddamar da cikakken bincike kan kisan da ake yi wa sojan na kashe direban, wanda shi ne ya haddasa rufe hanyar tun da farko.

%d bloggers like this: