Wani direban mota ya yi ajalin wani dan bunburutu mai suna Abdullahi Mohammed da ’ya ’yansa biyu a Abuja.
Wannan lamari ya faru ne a mahadar Dei-Dei da ke kan babbar hanyar Zuba zuwa Abuja a ranar Litinin.
- Al-Zawahiri: Wane ne shugaban Alka’idan da Amurka ta kashe?
- ‘Akwai ’yan majalisa da dama masu goyon bayan yunkurin tsige Buhari’
Wani mai suna Abubakar wanda lamarin ya faru a idonsa ya ce, mutum da ke sana’ar sayar da fetur a bakin titi da kuma ’ya’yansa biyu na tafe ne kan wani mashin lokacin da hadarin ya faru.
“Wadanda lamarin ya rutsa da su sun nufi inda suke sana’arsu ce yayin da direban motar da ya yi aron hannu ya cimm masu, lamarin da ya hallakasu baki daya a kusa da wata unguwa da ake ka kira Dantata.
“Mai motar na kan hanyarsa ne ta zuwa Kubwa yayin da motar ta kwace ta kuma tsallaka inda mutanen ke tafe ta kuma buge su, wanda hakan ta sa ko shurawa ba su yi ba, suka mutu.”
Elizabeth Benedict, Shugabar Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) da ke Zuba, ta tabbatar da faruwar lamarin tare da danganta aukuwar hadarin da gudun wuce sa’a na direban motar.
A cewarta, tuni rundunar ‘yan sanda da ke Zuba ta shiga lamarin bayan su mika shi a hannunta.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, har an binne mamatan a bisa tanadi na addinin musulunci.