Wani matashi mai suna Jude Nnabuife, ya bayyana yadda wani direba ya sace masa mota, kwana daya bayan ya dauke shi aiki, inda ya yi niyyar sayar da motar amma bai samu sa’a ba.
Nnabuife, wanda mazaunin Gwarimpa ne, ya ce ya dauki Mathew Agbe, dan shekara 30 a ranar 6 ga watan Oktoba na bana, sannan kuma ya fara aiki a ranar 9 ga watan Oktoba, amma abin mamaki, sai ya gudu da motar washegari. “Ya tambayi dayan direban ya ba shi mabudin dayan motata kirar Kia Cerato, wai zai je ya wanke ta amma jim kadan da karbar mabudin, sai ya kashe wayarsa.
“Sai na kira DPO na Gwarimpa da bangaren kula da satar motoci na SARS. Bayan kwana 6, sai ’yan sanda suka kira ni, suka ce in zo an gano motar, kuma an kama wanda ake zargi.” inji shi.
“Ya so ya sayar da motar ne a kan kudi Naira dubu 200 a wajen garejin Apo, motar da na saya a kan kudi Naira Miliyan 3.5.”
Kamar yadda ’yan sanda suka bayyana, wanda ya je garejin sai ya nuna cewa zai sayi motar ne, sai ya boye ya kira su. Koda suka isa wajen, sun samu kayansa a cikin motar, wanda ke nuni da cewa ya so da sayar da motar ne, sai ya bar garin.
Wanda ake zargin, ya ce shi ba sace motar ya yi ba, kawai ya yi amfani da ita ya daukan fasinja ne, sai ’yan sanda suka kama shi. “Kawai na dauki motar ne na je na sayo wasu kaya, da zan dawo sai na dauko fasinja domin na samu wasu ’yan kudade; sai ’yan sanda suka kama ni wai saboda motar ba ta daukar fasinja ba ce. Sai suka rike motar na tsawon kwana shida, har sai ranar da na samu na yi beli.
“Bayan na karbi motar, sai na kai ta wajen gyaran mota na Apo sai na sha giya na bugu a wajen, kawai ban ankara ba sai na ga ’yan sanda sun zo sun tafi da ni,” inji shi.
Da aka tambaye shi abin da ya sa bai kira maigidansa ba a lokacin da ake ta wannan dambarwar, sai ya ce “Dare ya yi a ranar, kuma na riga na bugu.”
Mathewa yana cikin wadanda ake zargi su 37 da Kwamishinan ’yan sandan Abuja, Sadik Bello ya gabatar wa manema labarai a ranar Talata da ta gabata.