Wani direban motar haya ya gano wanda ya yi garkuwa da shi a cikin fasinjojin da zai dauka zuwa Kano a tashar mota da ke unguwar Kwanawa a Karamar Hukumar Dange Shuni, Jihar Sakkwato.
An yi garkuwa da direban ne a hanyar Kankara a cikin Jihar Katsina a hanyarsa ta dawowa daga Kano kusan wata biyu da suka wuce, inda ya kwashe sati uku a tsare kafin a sake shi bayan an biya kudin fansa.
- Yadda ’yan sanda ke ‘garkuwa da mutane’ a Kano
- Yadda ’yan Najeriya suka fusata da kisan manoma a Borno
- Zabarmari: A gabana aka yi ta yanka ’ya’yana —Mahaifi
Wanda ake zargi ya shiga hannu ne a bayan ya shiga mota zuwa Kano, ba tare da sanin cewa ya ta ba yin garkuwa da direban motar ba.
Majiyarmu ta ce da ganin wanda ake zargin, direben ya gane shi, kuma nan take ya sanar da shugabannin kungiyar direbobi ta NURTW.
Daga nan kungiyar ta sauya direban motar da wani, bayan sun fita cikin tasha sun kai garin Shuni, ’yan sanda suka tare motar aka kama wanda ake zargi.
Da ’yan sanda suka titsiye wanda ake zargin ya amsa cewa yana cikin masu garkuwa da mutane karkashin wani gungu da ake kira Hadari.
Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, DSP Muhammad Sadik ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce ana kan bincike.