Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ya fahimci mutane suna kiransa ‘Baba Go Slow’ wato mai tafiyar hawainiya ne saboda yana yaki da rashawa bisa tsarin da mulkin dimokuradiyya ya shimfida.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da wadansu mazauna Abuja suka kai masa gaisuwar Barka da Kirsimeti a karkashin jagorancin Ministan Abuja a ranar Talatar da ta gabata.
Shugaba Buhari ya ce ya yi watsi da bin tsarin soja wajen yaki da rashawa. “Lokacin da nake sauri an kama ni an tsare, to yanzu kuma saboda me zan yi sauri?” inji shi.
Ya ce tsarin dimokuradiyya ne ya zo da haka ba Baba ba, “Duk da haka ba zan dakatar da farautar wadanda suka saci kudaden al’ummar da aka damka musu amana ba,” inji shi.
A yayin da yake shirin kaddamar da yakin neman zabensa na 2019, Shugaban ya nanata manyan abubuwan da gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali a kansu.
Ya ce yakin neman zaben nasa zai karkata akala ne ga nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fannin tsaro da tattalin arziki da kuma yaki da rashawa.
“Za mu tafi yankunan kasar nan domin tunatar da su alkawuran da muka dauka a 2015 musamman fannoni uku, tsaro da tattalin arziki da kuma yaki da rashawa,” inji Shugaban Kasar.
Ya ce mutanen Arewa maso Gabas sun tabbatar da nasarar da aka samu a yaki da Boko Haram. Sai dai kuma ya ce gwamnatinsa a shirye take wajen kawo karshen matsalolin ’yan bindiga da barayin shanu da masu garkuwa da mutane da ke addabar jihohin yankin Arewa maso Yamma.
Kwana guda kafin wannan ne al’ummar Zamfara suka gudanar da zanga-zangar nuna damuwa da yawan kashe-kashen mutane da ake yi a jihar.
Duk da sojoji da ’yan sandan da aka tura Jihar Zamfara, har yanzu al’ummar jihar suna cewa babu wani sauki kan matsalar tsaron da suke fuskanta. An dai shafe shekaru ana ci gaba da samun matsalolin satar mutane don neman kudin fansa da hare-haren ’yan bindiga a sassan Jihar Zamfara.