✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dimokuradiyya ce ta yi tasiri a zaben Osun —Buhari

Buhari ya taya Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP murnar lashe zaben.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce dimokuradiyya ce ta yi tasiri a zaben gwamnan Jihar Osun da aka gudanar a ranar Asabar.

Shugaban ya bayyana hakan ne cikin wani sakon taya Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP murnar lashe zaben.

Cikin sakon da Buhari ya wallafa a shafinsa na Facebook a Lahadin nan, ya ce bayyana cewa al’ummar Jihar Osun sun nuna ra’ayinsu ta hanyar jefa kuri’a.

A cewarsa, dole ne a girmama abin da mutane suke so kamar yadda tsari na dimokuradiyya ya yi tanadi.

“Wannan shi ne abin da dimokuradiyya ke nufi: mutunta muradun jama’a,” in ji Buhari.

Shugaban ya bayyana cewa gudanar da zaben da aka yi lafiya wata alama ce da ke nuna cewa an samu ci gaba a kokarin da ake yi na kara inganta harkokin zabe a Najeriya.

Ya yaba da yadda aka samu hadin kan Hukumar Zabe da jami’an tsaro da jam’iyyu da ’yan jarida da kungiyoyi masu zaman kansu da masu zabe.

“Yadda aka samu nasarar gudanar da zaben lafiya wata alama ce da ke nuna ci gaban hadin kan masu ruwa da tsaki wajen kara inganta harkar zabe a Najeriya.”

Shugaban ya kuma kara jaddada aniyarsa ta gudanar da ingantaccen zabe a lokacin mulkinsa.