Manoma suna fuskantar barazana a bakin Kogin Ringim da ke karamar Hukumar Ringim a Jihar Jigawa sakamakon mamaye bakin kogin da dillallan kwaya da wiwi suka yi.
Shugaban karamar hukumar Malam Abdullrahid Illah Ringim ya bayyana haka lokacin da yake jawabi a wajen taro da karamar hukumar ta shirya domin yaki da masu sha da sayar da miyagun kwayoyi a karamar hukumar.
Malam Illah Ringim ya ce yanzu haka karamar hukumar ta samu jerin sunayen mutanen da ake zargin dillalan wiwi da kwaya ne su 57 da suke karamar hukumar tare da samun labarin inda suke boye.
Shugaban ya nuna damuwa game da yadda ake samun karuwar masu sayar da miyagun kwayoyi da wiwi da masu tu’ammali da su a karamar hukumar tasa.
Ya ce hakan yana kai matasa ga aikata miyagun ayyukan da ake rasa rayuka a wasu lokuta. Ya ce ya zama dole a taka wa lamarin birki kafin ya kai ga wani hali, inda ya ce karamar hukumar za ta hada kai da jami’an tsaro don magance hakan.
Malam Illah Ringim ya ce karamar hukumar za ta bai wa jami’an tsaro umarnin kama duk wanda ke sayar da kwaya ko wiwi ko masu shansu, domin raba karamar hukumar da miyagu.”Babu ruwanmu da dangantaka ko matsayin mahaifin yaro duk wanda aka kama doka za ta yi aiki a kansa babu maganar siyasa,” inji shi.
Sai ya soki lamirin wadansu iyaye musamman mata da idan aka kama ’ya’yansu kan zargin aikata laifi suke suke sanya mazansu a gaba sai an yiwo belin ’ya’yan. Ya ce hakan suna taimakawa ne wajen kangarewar ’ya’yan, ba gata suke yi musu ba.
Shugaban ya nuna damuwa kan yadda aka samu labarin wani mau shekara 55 bisa zargin yi wa yarinya ’yar wata hudu fyade, bayan ya sha kwaya a garin na Ringim. Sai ya yi alkawarin ladan Naira dubu 30 ga duk wanda ya tona asirin dillalin kwaya ko na wiwi a karamar hukumar.
Ya ce sun kafa kwamatin sa-ido na mutum 12 a unguwanni da ke karamar hukumar domin kai musu bayanan sirri don dakile ayyukan barna. Kwamitin a karkashin Malam Musa Sale ya samu ne sakamakon wani taron bita da aka shirya wa matasa kan illar sha da tu’ammali da miyagun kwayoyi a yankin.