Wata dillaliyar katin waya a garin Madalla da ke Jihar Neja, mai suna Rita bincent ta yi asarar kudi da kati da aka kiyasa sun haura Naira dubu 700, ga ’yan damfara.
Lamarin, wanda ya faru a ranar Alhamis ta makon jiya ya sanya matar cikin kidima, inda ta rika sintirin neman dan damfarar tare da wani dan acaba da ta dauki shatarsa.
Da take yi wa wakilinmu bayani a kan al’amarin, matar ta yi ikirarin cewa mutumin ya zo shagonta ne da misalin karfe 11:30 na safe inda da farko ya tambaye ta wata da suka yi aiki a baya. “Na shaida masa cewa ba ta tare da mu a yanzu.”
A cewarta, mutumin yana sanye da shat samfurin wani kamfanin sadarwa da wandon jins da kuma hula hana Sallah tare da kwamfutar hannu, “Da farko ya ce zai taimaka mana da tebura da lemomi don raba su ga abokan huldarmu a matsayin kyutar kamfani. Na ce shagonmu a kullum yana karbar sautun katin waya na kamfanoni daban-daban na Naira dubu 700, kuma nan take na dauko cinikin da na yi na ranar na Naira dubu 60 da kuma na wunin da ya gabace shi Naira dubu 50 na mika masa tare da tarin katin da ke wajena ba tare da na san abin da nake yi ba.”
A lokacin da wakilinmu ya koma shagon Rita a ranar Talatar da ta gabata, ya samu ta koma harkarta kamar yadda ta saba. Da ya tambaye ta game da mai shagon ta bayyana cewa maigidan nata ya yi tafiya kuma ba zai dawo ba sai washegari.
Babban jami’in ’yan sanda na Madalla S.P Abdulkarim Ibrahim wanda ya tabbatar da faruwan lamarin, ya kara da cewa bayan wadda aka damfarar ta shigar da kara a ofishin, an bukaci ta kawo bayanin adadin katin da aka yi mata damfarar, sai dai har zuwa wannan lokacin ba ta sake komawa wurinsu da karin bayanin ba.
Dillaliyar katin waya ta ce an damfare ta Naira dubu 700
Wata dillaliyar katin waya a garin Madalla da ke Jihar Neja, mai suna Rita bincent ta yi asarar kudi da kati da aka kiyasa sun…