An kama wani mai kerawa da kuma yi wa bata-gari safarar makamai.
’Yan sanda da suka cafke mutumin wanda ya yi fice wurin sayar wa kungiyoyin asiri bindigogi, sun kuma gano cewa dan kungiyar matsafa ta Bobos ne.
- ’Yan bindiga sun saki sabon bidiyon daliban Kwalejin Afaka
- An kai hari a rugar Fulani a Abuja
- An cafke Basarake da iyalansa kan zargin garkuwa da mutane
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya ce, “Bayan samun bayanan sirri daga al’umma ne aka cafke matashin mai shekara 28, wanda ya kware wurin kerawa da kuma sayar da bindigogi ga kungiyoyin asiri.”
Ya ce wanda ake zargin ya sayar da bindigogi da ba a san iyakarsu ba ga ’yan fashi a Jihar ta Bayelsa.
“Jami’an binciken kwakwaf na bin sawun sauran ’yan kungiyoyin matsafan da suka sayi makamai a wurinsa.
“Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bayelsa, Mike Okoli, ya roki jama’ar jihar da suka ci gaba da bayar da hadin kai da bayanai ga Rundunar domin yakar ayyukan laif a Jihar.”