Kungiyar Dillalan Jakuna ta Najeriya na neman Hukumar Kwastam ta Kasa ta biya ta diyyar Naira biliyan daya saboda kwace mata naman jakin da ta yi.
Kungiyar dai ta zargi Kwastam da kwacewa tare da mika nama da fatun jakunanta ga Hukumar Killace Kayayyakin Amfanin Gona ta Najeriya (NAQS) a kwanakin baya.
- Gwamnatin Taliban ta zartar da hukuncin kisa a cikin masallaci
- Tsananin zafi ya yi ajalin kusan mutum 100 a India
Tuni dai hukumar ta NAQS ta lalata kimanin buhu 414 na naman jakin, wanda aka yi hasashen darajarsa ta kai kimanin Naira miliyan 200, wanda hukumar Kwastam ta kama ranar 19 ga watan Mayu a Jihar Kebbi.
Kwastam dai ta yi zargin naman na kan hanyarsa ce ta zuwa kasuwar Ochanja da ke Jihar Anambra, inda daga can za a wuce da shi kasar China da sauran kasashe.
Sai dai dillalan jakunan sun yi zargin cewa an kama kayan nasu ne saboda sun ki biyan cin hancin Naira miliyan daya da rabi da jami’an Kwastam din suka nema daga hannunsu domin su kyale a wuce da su.
A tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Najeriya (NAN) ta wayar salula ranar Talata, shugaban kungiyar dillalan, Ikechukwu Aniude, ya tabbatar da cewa suna neman diyyar, kuma ba za su lamunci ci gaba da kama musu naman ba.
A sassan Najeriya daban-daban na Najeriya dai, musamman a Kudancin kasar, mutane na cin naman jaki saboda saukinsa, sannan akan fitar da shi kasahen waje domin hada magunguna. (NAN)