Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Kasa (IPMAN) ta dakatar da yajin aikin da ta kudiri aniyar farawa daga ranar Talata ta hanyar rufe dukkan gidajen man da ke kasar nan.
Sakataren kungiyar na kasa, Alhaji Danladi Garba Pasali ne ya bayyana haka a yammacin Litinin.
- Babu hannunmu a tarwatsa zanga-zangar daliban Gidan Waya – Gwamnatin Kaduna
- Hatsarin mota ya lakume rayukan ’yan Najeriya 2,233 a wata 4
Tun da farko dai IPMAN ta yi barazanar rufe dukkan gidajen man da ke Najeriya daga ranar Talata matukar Gwamnatin Tarayya da Babban Sufeto ’Yan Sandan ba su dauki mataki kan rufe sakatariyar kungiyar da jami’an ’yan sanda da ke Abuja suka yi ba.
Kungiyar dai na zargin cewar rufe mata sakatariyar da aka yi ranar Juma’a da cewa ba ya kan ka’ida.
Alhaji Danladi Garba Pasali ya ce sun ta dakatar da yajin aikin ne sakamakon zaman da suka yi da hukumar gudanarwar Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) da wakilan Majalisar Tarayya da jami’an shaktwatar ’yan sanda ta kasa da kuma wakilan Fadar Shugaban Kasa a kan lamarin a ranar Litinin.
“Sakamakon abubuwan da muka tattauna da wadannan masu ruwa da tsakin, mun cimma matsaya kan ’yan kungiyarmu, su dakatar da wannan yajin aiki da muka tsara yi.
“Don haka, muna kira ga dukkan ’yan mambobinmu na shiyyoyi da jihohin kasar nan kan su dakatar da wannan yajin aiki da za ayi,” inji shi.