✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur

Yanzu matatun man ƙasar na aiki, kuma hakan zai sa farashin litar man fetur ya ci gaba da sauka.

Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Nijeriya IPMAN, ta musanta jita-jitar da ake yaɗawa ta ƙarin farashin litar man fetur a faɗin ƙasar.

IPMAN ta ce, yanzu matatun man ƙasar na aiki, kuma hakan zai sa farashin litar man fetur ya ci gaba da sauka.

A tattaunawarsa da Muryar Amurka, Shugaban IPMAN reshen Arewa maso Yamma, Bashir Salisu Tahir, ya musanta wannan zargi na karin farashin litar man fetur.

Ya kuma tabbatar da cewa babu wani mamban ƙungiyarsu da ya ƙara farashin litar man fetur a ƙasar.

Tahir, ya ce “yanzu kasuwa ce ke samarwa kanta farashi, kuma batun ƙarin farashin litar man fetur a ƙasar babu shi.”

Shugaban na IPMAN ya ƙara da cewa “duk da cewa an samu ƙarin farashin man dizel a ‘yan kwanakin nan, farashin sa ne ya tashi a kasuwa, kuma idan farashinsa ya sauko, to tilas za a sayar da shi a farashi me sauki.”

Tahir, ya kara da cewa “yanzu matatun man kasar sun fara aiki, don haka farashin man fetur zai sauko.”

Kawo yanzu dai ’yan Nijeriya na ci gaba da hanƙoron ganin matakan da gwamnati ke ɗauka za su kawo musu sauƙin rayuwar da janye tallafin man fetur ya jefa su a ciki.