✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

IPMAN da Dangote Sun cimma yarjejeniya kan fara dakon mai

Ƙungiyar ta ce cimma yarjejeniyar za ta sa a samu man fetur mai rahusa a faɗin Najeriya.

Ƙungiyar Dilallan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN), ta cimma yarjejeniya da Matatar Dangote kan fara dakon man fetur kai-tsaye daga wajen su.

Yarjejeniyar ta samu ne bayan makonni da aka ɗauka ana tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu kan samar da man fetur a sauƙaƙe kuma a farashi mai rahusa.

Da yake magana da manema labarai a Abuja, Shugaban IPMAN, Abubakar Garima, ya ce yarjejeniyar za ta inganta haɗin gwiwa tsakaninsu, wanda zai taimaka wajen samar da isasshen man fetur mai rahusa a faɗin ƙasar.

Garima, ya yi kira ga mambobin IPMAN da su bai wa matatar Dangote goyon baya domin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.

“Bayan ganawa da Aliko Dangote da mahukuntansa a Legas, muna farin cikin sanar da cewa Matatar Dangote za ta samar wa IPMAN da man fetur, dizal, da kalanzir kai-tsaye don rabawa zuwa manyan rumbunan ajiyarmu da wuraren sayarwa,” in ji shi.

Ya kuma shawarci mambobin IPMAN da su dogara da Matatar Dangote da matatun man Najeriya, wanda zai ƙara samar da ayyukan yi da kuma tallafa wa manufofin cigaba na Shugaba Bola Tinubu.

Tun da farko a watan Nuwamba, IPMAN ta bayyana cewa tsadar jigilar mai daga Matatar Dangote ta sa wasu dilallai neman mai rahusa.

Rashin cimma yarjejeniya tsakanin IPMAN da Dangote ya janyo tsaiko da ƙalubale wajen samar da man fetur a baya.