Shahararren dan kwallon duniya kuma dan asalin Ajantina Diego Maradona ya yi tiyata a fuskarsa inda ya canza mata kamannin kuma ya koma kamar saurayi dan kimanin shekara 24.
Tsohon dan kwallon ya yanke shawarar yin tiyaya a fuska don ya canza kamanninsa ne don ya faranta wa budurwarsa mai suna Rocio ’yar kimanin shekara 24 ganin yadda take daukarsa kamar wani tsoho, al’amarin da ya sa ba ta sakin jiki idan suna tare a mafi yawan lokuta.
Maradona da yanzu haka yake da shekara 54 ya ce ya yanke shawarar a yi masa tiyaya a fuska ne don a canza masa kamanni ya koma kamar saurayi dan shekara 24 don ya yi kafada da kafada da budurwasa ’yar kimanin shekara 24.
Kafar sadarwar Mirror ta kalato cewa a lokuta da dama Maradona da budurwar tasa sun sha samun sabani a kan yadda yake matukar kaunarta amma ita kuma take daukarsa a matsayin dattijo.
Rahotanni sun tabbata ko a bara sai da jami’an tsaro suka yi garkuwa da Rocio a kan zargin ta sace wa Maradona makudan kudi da sarkokin gwal a gidansa da ke Dubai amma daga baya ya yafe mata kuma ya nemi su cigaba da soyayya.
Sai dai dudurwar ta amince ta ci gaba da yin soyayya da shi a halin yanzu ne bayan ya yi wa fuskarsa kwaskwarima inda ya koma kamar wani saurayi dan kimanin shekara 24. Ta ce ta yafe duk laifin da Maradona ya yi mata a baya kuma ta sha alwashin rike shi da gaskiya har tsawon rayuwarta.
Sai dai rahoton bai ambaci kudi da kuma wurin da aka yi wa Maradona kwaskwarima a fuska ba amma sai a halin da ake ciki Maradona yana zaune a Dubai ne a matsayin kocin wani kulob al’amarin da wasu ke hasashen a can ne aka yi masa aikin a fuska.