✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Diego Maradona: Napoli ta sauya wa filin wasanta suna

Kungiyar kwallon kafa ta Napoli ta sauya sunan filin wasanninta daga San Paolo Stadium zuwa Diego Armando Maradona Stadium domin karrama tsohon dan wasanta, Diego…

Kungiyar kwallon kafa ta Napoli ta sauya sunan filin wasanninta daga San Paolo Stadium zuwa Diego Armando Maradona Stadium domin karrama tsohon dan wasanta, Diego Maradona da ya mutu a makon jiya.

Magajin garin Naples, Luigi De Magistris, shi ne ya rattaba hannu kan wannan sabuwar doka ta sauya wa filin wasannin suna a wata sanarwa da Gwamnatin yankin na Campania ta fitar.

Hukumomin kungiyar da kuma shugabanta, Aurelio De Laurentis ne suka gabatar da bukatar sauya wa filin wasannin suna awanni 12 da mutuwar Maradona a ranar 25 ga watan Nuwamba.

Maradona, wanda Duniya ke kallo a matsayin daya daga cikin shahararrun ‘yan kwallon da babu kamarsu, shi ne ya jagoranci kungiyar Napoli da ta lashe gasar Serie A har kawo biyu a tsawon shekaru bakwai da ya shafe a kungiyar a tsakanin shekarar 1984 zuwa 1991.

Kazalika ya jagoranci tawagar kwallon kafar Argentina a matsayin Kyaftin da ta lashe kofin duniya a shekarar 1986 a Mexico.