Ko me ya hana shugaban kasa Bola Tinubu mika sunayen ministoci daga Jihar Kano da mahaifarsa Legas da wasu jihohi tara ga Majalisar Dokoki ta Kasa domin tantancewa.
Hakan da shugaban ya yi a jerin sunayen da ya mika a ranar Alhamis da wa’adin da doka ta kayyade masa ya haifar da ce-ce-ku ce.
- Juyin mulkin Nijar: An kai hari hedikwatar Bazoum
- Kotu ta kori bukatar DSS na neman ci gaba da tsare Emefiele
Shugaban ya mika sunayen ministoci 28 daga 25 daga cikin jihohi 36 da ke Najeriya, inda jihohin Bauchi, Katsina da Kuros Riba suka samu mutum biyu kowannensu.
Wadanda aka mika sunayen nasu sun hada da mambobin kwamitin yakin neman zaben Tinubu a jam’iyyar APC, da kuma kwararru.
Jihohi 11 da shugaban bai ayyana sunayen ministoci ba sun hada da mahaifarsa Jihar Legas, da kuma Kano, wadda ta yawan al’umma kuma kuri’u a Arewacin Najeriya. Sai kuma Kebbi da Filato da Yobe da Adamawa da Gombe da Yobe da Zamfara da Osun da kuma Bayelsa.
Kebbi dai ita ce jihar tsohon shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar, Atiku Bagudu; Filato kuma jihar daraktan yakin neman zabensa, tsohon Gwamna Simon Lalong. Adamawa kuwa jihar na hannun damansa kuma Mashawarci kan Tsaron Kasa, Nuhu Ribadu da dai sauransu.
Ina makomar Ganduje?
Aminiya ta gano cewa rashin ayyana sunan minista daga Jihar Kano na da nasaba da rashin tabbas game da makomar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, wanda wasu ke cewa shi ne zabin Tinubu.
Amma wata majiya mai tushe ta ce cewa kawancen Tinubu bayan da tsohon uban gidan Ganduje wanda yanzu ba sa ga-maciji, kuma dan takarar shugaban kasan Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso bayan zabe, a hannu guda; da kuma murabus din da Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi, wanda ya samar da gibi a shugabancin jam’iyyar a daya hannun, suna daga cikin dalilan rashin tabbas game da makomar Ganduje a jerin sunayen ministoci.
Kwanaki kadan bayan murabus din Abdullahi Adamu ne aka fara rade-radin cewa Ganduje ne zai mayye gurbinsa, lamarin da wasu ke ganin shi ne silar rashin ayyana shi a jerin ministocin da Tinubu ya mika wa Majalisa.
Tun a makon jiya wani jigo a APC a Jihar Kano ya shaida mana cewa rahoton da suka samu ya nuna cewa babu Ganduje a cikin jerin sunayen ministoci, amma za a ba shi damar maye gurbin tsohon shugaban jam’iyyar.
“Mu mun ma fi son haka, domin idan Baba (Ganduje) ya zama shugaban jam’iyya, kai-tsaye za a rika damawa da shi a jam’iyya, baya ga damar da yake da ita na dorewar kusancinsa da shugaban kasa,” a cewarsa.
Kwankwaso fa?
Babban fargabar jagororin APC a Kano ita ce shirin da suka ga bayan zaben shugaban kasa Tinubu ya fara yi da Kwankwaso, wanda jam’iyyarsa ta NNPP ce take mulkin jihar, inda suke zargin hakan na iya tasiri wajen ba da kujerar ministan da shguaban kasar zai yi wa jihar.
Yawancinsu na ganin idan har shugaban kasan ya ba wa bangaren Kwankwaso, hakan zai illata jam’iyyar tare da rura wutar rikicin jagoranci a nan gaba.
Tasiri a siyasa
Amma waa majiya ta shaida mana cewa baya ga batun mukamin minista, Tinubu yana la’akari da tasirin da hakan zai yi a siyasa a zaben 2027.
“Akwai kuma batun kararrakin zabe da ke gaban kotu; don haka yana bukatar nagartattun mutane a jihohi, ba ma Kano kadai ba, wadanda ko da za a sake zabe, za su iya kawo masa kuri’un da yake bukata.”
Mataimakin shugaban APC na jihar, Shehu Maigari, ya shaida mana cewa jam’iyyar na da nagartattun mutane da suka taka muhimmiyar rawa wajen ganin Tinubu ya ce zaben shugaban kasa.
“Akwai irin su tsohon mataimakin gwaman Ahmed Tijjani Gwarzo, wanda ke tare da Asiwaju tun suna tsohuwar jam’iyyar ACN.
“Zan iya bugun kirji da cewa in banda jagoranmu Ganduje, babu wanda ya kai shi ba da gudummawa domin ganin Tinubu ya ci zabe.
“Ga irin su tsohon sakataren gwamnati Rabiu Suleiman Bichi, da irin su tsohon ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau; karamin takadiri ke nan na wadanda suka cancanta,” in ji shi.