Kungiyar kwallon kafa ta Napoli ta sauya sunan filin wasanninta daga San Paolo Stadium zuwa Diego Armando Maradona Stadium domin karrama tsohon dan wasanta, Diego Maradona da ya mutu a makon jiya.
Magajin garin Naples, Luigi De Magistris, shi ne ya rattaba hannu kan wannan sabuwar doka ta sauya wa filin wasannin suna a wata sanarwa da Gwamnatin yankin na Campania ta fitar.
- Matata ta auri dan sanda a asirce a kan aurena
- Kotun Daukaka Kara ta tabbatar wa Maryam Sanda hukuncin kisa
- A daure Maina a gidan kaso har sai bayan shari’arsa — Kotu
Hukumomin kungiyar da kuma shugabanta, Aurelio De Laurentis ne suka gabatar da bukatar sauya wa filin wasannin suna awanni 12 da mutuwar Maradona a ranar 25 ga watan Nuwamba.
Maradona, wanda Duniya ke kallo a matsayin daya daga cikin shahararrun ‘yan kwallon da babu kamarsu, shi ne ya jagoranci kungiyar Napoli da ta lashe gasar Serie A har kawo biyu a tsawon shekaru bakwai da ya shafe a kungiyar a tsakanin shekarar 1984 zuwa 1991.
Kazalika ya jagoranci tawagar kwallon kafar Argentina a matsayin Kyaftin da ta lashe kofin duniya a shekarar 1986 a Mexico.