✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Diego Costa zai bar kungiyar Atletico Madrid

Kungiyar ta amince da warware yarjejeniyar ne, bayan da Costa ya aike mata da bukatar hakan a rubuce.

Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta sanar da warware yarjejeniya tsakaninta da dan wasanta, Diego Costa a ranar Lahadi.

Costa ne ya aike wa da kungiyar ta Atletico Madrid bukatar hakan, ita kuma kungiyar ta amince bayan duba bukatar ta sa.

Shekara ta 2020 dai ta kawo wa Costa tsaiko da koma baya, inda ya sha fama da jinyar raunuka da ya samu, daga baya-bayan kuma ya harbu da cutar COVID-19.

Diego Costa

Sanarwar ta kawo karshen zamansa a kungiyar a karo na biyu.

Costa ya bar kungiyar zuwa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a 2014, inda ya zura kwallaye 64 a wasanni 134 da ya buga mata.

Sai dai bayan dawowarsa kungiyar a karo na biyu, Costa ya zura kwallaye 19 a cikin wasanni 81 da ya buga.