Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta sanar da warware yarjejeniya tsakaninta da dan wasanta, Diego Costa a ranar Lahadi.
Costa ne ya aike wa da kungiyar ta Atletico Madrid bukatar hakan, ita kuma kungiyar ta amince bayan duba bukatar ta sa.
- Messi ya share tarihin da Pele ya kafa a kwallon kafa
- Ronaldo ya lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasan Karni
- Diego Maradona: Napoli ta sauya wa filin wasanta suna
- PSG da Atletico Madrid sun tsallaka zagaye na gaba
Shekara ta 2020 dai ta kawo wa Costa tsaiko da koma baya, inda ya sha fama da jinyar raunuka da ya samu, daga baya-bayan kuma ya harbu da cutar COVID-19.
Sanarwar ta kawo karshen zamansa a kungiyar a karo na biyu.
Costa ya bar kungiyar zuwa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a 2014, inda ya zura kwallaye 64 a wasanni 134 da ya buga mata.
Sai dai bayan dawowarsa kungiyar a karo na biyu, Costa ya zura kwallaye 19 a cikin wasanni 81 da ya buga.