Kocin kulob din Arsenal da ke Ingila Arsene Wenger ya tabbatar da raunin da dan kwallon bayansa Mathiue Debuchy ya samu a wasan da suka yi da kulob din Manchester City a gasar rukunin Premier a ranar Lahadin da ta gabata.
Kocin ya ce rahotanni da ya samu daga Likitocin kulob din sun tabbatar masa dan kwallon ba zai sake buga wa kulob din wasa ba har har na tsawon watanni uku.
Debuchy, dan kimanin shekara 29, ya fadi kasa ne shi kadai a yayin da wasa ke gudana a tsakanin kulob din da na City al’amarin da ya sa aka dauke shi a makara zuwa asibiti. A asibitin ne aka tabbatar ya samu matsala a kokon gwiwarsa da hakan ya sa zai shafe kimanin wata uku yana jinya.
An tashi wasan ne ci 2-2.
Debuchy zai shafe watanni uku yana jinya
Kocin kulob din Arsenal da ke Ingila Arsene Wenger ya tabbatar da raunin da dan kwallon bayansa Mathiue Debuchy ya samu a wasan da suka…