✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daya daga cikin daliban Chibok ta tsere daga hannun Boko Haram

Ruth da mijinta sun mika kansu ga sojoji a garin Bama.

Gwamna Babagana Umar Zulum na Jihar Borno ya karbi Ruth Pogu, daya daga cikin ’yan mata fiye da 200 da mayakan Boko Haram suka sace a garin Chibok a shekarar 2014.

Wata sanarwa da Mallam Isa Gusau, mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin sadarwa ya fitar, ta ce Pogu da wani mutum da ya bayyana kansa a matsayin mijinta sun mika wuya a garin Bama.

  1. ’Yan Boko sune matsalar Najeriya — Sarkin Musulmi
  2. Najeriya ba irin su Atiku ko Tinubu take bukata ba a 2023 – IBB

“A ranar 28 ga Yulin 2021 ne Ruth ta mika kanta ga sojojin Najeriya ita da wani mutum da ta ce mijinta ne da ta aura a lokacin da suke tsare.

“A karkashin kulawar Zulum, jami’an tsaro da jami’an gwamnati sun boye sirrin abin da ke faruwa inda suka yi amfani da kwanaki 10 da suka gabata don tuntubar iyayenta da kungiyar iyayen ‘yan matan makarantar da suka bace don gano asalin ta,” in ji Gusau.

Gusau ya ce a yayin karbar Ruth da mahaifiyarta da danta a Fadar Gwamnatin jihar, Gwamna Zulum ya bukaci sauran iyayen daliban sakandaren ta Chibok da su ci gaba da fatan ganin ’ya’yansu.

“Zulum ya ce sake haduwa da Ruth abun a yaba ne ganin yadda aka same ta cikin koshin lafiya.

“Ruth da iyayenta, za su sake saduwa da juna bayan tsawon shekaru, inda za su maida hankali kan lafiyarta da kuma nema mata makoma.

“Gwamnan ya yi jaje ga tare iyalan wadanda har yanzu ke hannunsu kuma ya bukace su da su kasance masu kyakkyawan fata, yin addu’a da hadin kai tare da hukumomin tsaro,” in ji Gusau.

Shugaban kungiyar ’yan matan Chibok, wata kungiya ta dukkan iyayen da abin ya shafa, Yakubu Keki, ya bayyana farin cikin dawowarsu.

Keki ya yi godiya ga jami’an tsaro da duk wadanda ke ci gaba da nuna damuwa kan halin iyayen da aka sace ’ya’yansu mata ke ciki.

Ana iya tuna cewa, a daren 14 ga watan Afrilun 2014 ne mayakan Boko Haram suka afka wa makarantar Sakandiren Mata zalla da ke garin Chibok tare da sace ’yan mata fiye da 200.