✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daula Hotel: Kamfanin da ke gini na neman diyyar N10bn daga Gwamnatin Kano

Kamfanin Lamash Properties ya karyata cewa sayar masa da otel din Daula gwamnatin Ganduje ta yi

Kamfanin da Gwamnatin Jihar Kano ta rushe gine-ginen da yake yi a Daula Hotel bisa zargin an sayar masa ba bisa ka’ida ba, ya ce zai maka gwamnatin a kotu domin neman diyyar Naira biliyan 10.

Kamfanin mai suna ya Lamash Properties ya ce rushe gine-ginen da gwamnatin ta yi bayan an kammala kashi 90 dinsu, kama-karya ne da rashin adalci.

Lamash Properties ya bayyana cewa sabanin rade-radin da ake yadawa cewa Gwamnatin Gwanduje ta sayar masa da otel din ba bisa ka’ida ba, domin gwamnati ta ba shi kwangilar ne a shekarar 2020, bayan ta nemi kamfanoni su mika bukatar sake farfado da Daula Otel, bisa tsarin hadaka da ’yan kasuwa.

“Ba sayar mana aka yi ba, gwamnati ce ta ba mu izinin gina Daula Boutique Hotel da hadin gwiwarta, saboda haka wannan matakin, zai sanyaya gwiwar masu zuba jari,” in ji sanarwar da Daraktan Kasuwancin kamfanin, Alhaji Aliyu Abubakar, ya fitar.

Ya kara da cewa, “Babu wanda ya sanar da mu ko ya nemi bayani daga wurinmu daga bangaren gwamnati game da aikin, wanda hakan ya saba wa abin da aka sani a duniya, na sauraron bangaren wanda ake zargi.

“Lamash Properties yana daga cikin kamfanonin da suka gabatar da takarudnsu domin kwangilar hadin gwiwar, wadanda gwamnatin jiha ta tantance, kuma bayan mun yi nasara, Majalisar Zartarwa ta jiha ta ba da izini sannan aka ba mu takardar kulla yarjejeniyar hadin gwiwar, kafin muka fara aikin.

“Darajar filin da abin da Gwamnatin Kano za ta samu da daga cikin ribar shi ne Naira biliyan 2.297, wanda kuma shi ne aka gina otel mallakin gwamnatin jihar da shi, karkashin tsarin mallaka na hadin gwiwa.

“Bayan haka akwai banaren masaukai na alfarma guda 25 da kuma shakuna da ake ginawa domin farfado da Daula Hotel.

“A ranar 27 ga watan Mayu, 2023, Gwamnatin Ganduje ta kaddamar da otel din, wanda aka damka mata shi, a matsayin kasonta na aikin.

“Amma ranar 4 ga watan Yuni, 2023 Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranci rusa gine-ginen da aka kammala kashi 90, ciki har da bangaren da aka gina otel mai dakuna 90 mai suna Daula Boutique Hotel, da sauransu.

“Abin takaici ne  gwamnati ta rusa kadararta mai irin wannan daraja, wandda zai kawo mata kudaden shiga tare da rage zaman banza, musamman a irin wannan yanayi na rashin kudi da rashin ayyukan yi.

“Lauyoyinmu za su shigar da karar neman diyyar Naira biliyan 10 kan abin da muka kashe, da kuma neman ac hana gwamnatin daukar duk wani mataki da zai yi mana illa a wannan yarjejeniyar.”

Sanawar ta kuma bayyana kwarin gwiwar samun adalci a a gaban kotu.