✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

daukar malaman makaranta dubu 500:- A yi adalci

Ina fata a daidai wannan lokaci da mai karatu ya ke karanta wannan  makala, miliyoyin matasan kasar nan da suke fadi-tashin neman samun ayyukan yi,…

Ina fata a daidai wannan lokaci da mai karatu ya ke karanta wannan  makala, miliyoyin matasan kasar nan da suke fadi-tashin neman samun ayyukan yi, bayan sun kammala karatunsu a manyan makarantu, zuwa yanzu sun yi nisa da neman aikin koyarwa ko na koyon sana`o`i don dogaro da kai, a karkashin shirye-shirye gwamnatin tarayya ta jam`iyyar APC, a zaman cikasa alkawarinta ga `yan kasa. A karkashin wadannan shirye-shirye na samar da ayyukan yi akwai daukar Malaman Makarantu 500,000, da za a tura Makarantun Sakandare da na Firamaren kasar nan, mai sunan N-power. Sannan akwai na N-Knowledge, wanda shi kuma za a dauki matasa 25,000, da za a koyar da su fannin fasaha, ko in ce sana`o`in zamani, yayin da shiri na uku N-Power build, da za a horar da matasa 75,000 akan gine-gine da kere-kere da sauran ayyukan fasaha.
Aniyar shirye-shiryen uku da na ambata a sama da ma wadanda Gwamnatin APC din ta sha alwashin gabatarwa kamar yadda ta tanade su a kasafin kudin bana, bai wuce samar da ayyukan yi da kuma dogaro da kai don ganin bunkasar tattalin arzikin `yan kasa, musamman ga miliyoyin matasan kasar nan da suka kammala karatun manyan makarantu da ma wadanda ba su yi karatun ba, amma suna zaune shekaru aru-aru ba su da ayyukan yi suna ta gararamba. Wasu ma rashin ayyukan yi ya sa sun zama `yan daba ko `yan fashi da makami da sace mutane ko yin garkuwa da su da dai sauran ayyukan ta`addanci irn na fasa bututun man fetur da tsagerun `yankin Neja Delta suka dukufa akai.
Makalar yau din za ta mayar da hankali ne akan daya daga cikin wadannan shirye-shirye uku da na ambata a sama, wato shirin N-power, da za a dauki masu digiri ko babbar takardar difloma har dubu 500 aikin koyarwa na wucin gadin tsawon shekaru biyu. Za a rinka ba kowannensu Naira dubu 23, duk wata a zaman alawus. Tuni mataimaki na musamman akan kafofin yada labarai ga Mataimakin shugaban kasa Mista Laolo Akande, ya ba da sanarwar cewa daga ranar Lahadi 12 ga wannan watan na Yuni, duk mai sha`awa sai ya bude dandalin yanar gizo na npwer.gob.ng ya tura bukatar sa, amma kuma bai ambaci ranar da za a rufe neman ba. Tuni wadanda suka ziyarce wancan dandali suka tabbatar da cewa an hada shirye-shiryen uku ne a dandali daya, don haka zabi yana wajen mai nema.
Kamar yadda na fadi tun farko, ni a kan shirin samar da aikin koyarwa mai gurbi dubu 500, zan mayar da hankali, ba don komai ba, sai don yawan guraben da aka kebe da kuma irin muhimmancin da ilmi yake da shi a cikin rayuwar dan Adam, musamman ma a yau da ake ta kuka a kasar nan a kan fannin na ilmi ya yi mummunar tabarbarewa, tun daga kasa har sama. To, ganin wata gwamnati ta zo ta ce za ta tallafe shi daga tushe, tun da an ce malaman da za a dauka za su koyar ne a makarantun Firamare da na Sakandare, makarantun da ilminsu shi ne tushen ilmi boko, a kowace kasa.
Kafin in kai fagen da zan yi maganar yin adalci kan yadda za a dauki malaman, ya kamata in waiwayi irin dimbin kudin da gwamnatin za ta kashe a cikin shirin da ake kyautata zaton zai jika hantar miliyoyin mutanen kasar nan ta fannoni daban-daban. Alal misali a karkashin wannan shiri za a bai wa kowane malami da ya yi nasara shiga shirin na`urar Kwamfuta, da za ta kunshi irin yadda tsarin koyarwar zai kasance da kuma irin horon da malami zai samu a cikin tsawon shirin na shekaru biyu. Mu kaddara kowace na`ura za a sayota a kuma sa ma ta bayanan da ake magana, ta tashi akan N100,000. Ka ga ke nan mai karatu a kan na`urorin kwamfutan dubu 500, gwamnati za ta kashe Naira biliyan 50, na`urorin da za a bai wa kowane malami kyauta a karshen shirin.
Idan ka dawo akan alawus din Naira dubu 23, da za a rinka bai wa kowane malami duk wata, kiyasi ya kama a kan kowane wata daya gwamnatin za ta rinka kashe Naira biliyan 11 da rabi , ya yin da a kowace shekara daya gwamnatin za ta rinka biyansu Naira biliyan 138. Jimlar abin da za ta kashe a shekarar farkon shirin za su kasance Naira biliyan 188, a shekara biyu kuwa za su tashi a kan Naira biliyan 326, wato idan ka hada kudun na`urorin kwamfuta da alawus din shekaru biyu na shirin. Mai karatu kasan wadannan ba kananan kudi ba ne, don kuwa ko da a kan na shekara daya ka tsaya, sai ka kewaya jihohin kasar nan da dama ba ka samu masu yin kasafin kudin da ya kai Naira biliyan 188 a shekara ba.
Ka ga ashe ke nan lallai akwai bukatar a tsaya a yi rabon cikin kamanta gaskiya da adalci, ko dai a raba  daidai tsakanin jihohi a kan yawan Majalisun kananan Hukumomi, ko ma na jihohin shiyyar Arewa maso Yamma da na shiyyar Arewa maso Gabas, nasu kason malaman ya fi yawa, domin kuwa a kullum alkalumman da Hukumar kididdiga ta kasa take bayarwa a kan talauci da rashin ayyukan yi, na tabbatar da cewa mutanen jihohin da ke cikin wadancan shiyoyi biyu, su suka fi na sauran shiyoyin kasar nan hudu fama da talaucin. Har yanzu dai babu wani tartibin bayani daga mahukuntan da aiwatar da shirin ya rataya a wuyansu a kan yadda za a raba wadancan gurabe dubu 500, da na sauraren shirye-shiryen biyu masu matasa dubu 25  da 75.
Amma a kaddara cewa raba daidai za a yi tsakanin jihohin kasar 36, da Abuja babban birnin tarayya, ke nan kowace jiha za ta tashi da yawan malaman da za a dauka, `dubu 13 da 513, ke nan. Ka gani mai karatu Jihar Kano mai mutane kusan miliyan 16, cikin kananan Hukumomi 44, zai kasance kowace karamar Hukuma ta za ta samu malamai 307, yayin da Jihar Bayelsa mai mutanen da ba su wuce miliyan uku a cikin kananan Hukumomi takwas ba, inda kowace karamar Hukumarta za ta tashi da Malamai  dubu da 689. Haka labarin zai kasance a cikin rabon, karancin majalisun kananan hukumominnka yawan Malaman da za a dauka, yawan al`ummarka da majalisun kananan hukomominka karancin Malaman da za a dauka a jihar ka.
Ka ga ke nan zai kasance kullum ana kara wa marar karfi, karfi  yana tumbatsa, mai karfi kuma ana kara raunana shi, talauci yana kara afka masa. Tun da dai batun dimokuradiyya ake, wanda ke aiki da yawan jama`a, to, ya ci kuwa dukkan irin mukamai da wasu ayyukan romon dimokuradiya da za a raba a kasar nan a rinka la`akari da hakan, musamman ga wannan gwamnatin da yawan jama`ar ya yi babban tasiri wajen kawo ta akan karagar mulki. Yanzu kuma ya kamata a fara. Ina kuma fatan dukkan shirye-shiryen da za su jika hantar talakawan kasa da niyyar saukaka musu kuncin rayuwar da suke ciki da wannan gwamnatin ta yi aniyar aiwatarwa a kasafin kudin bana, to, gwamnatin za ta mayar da hankalin wajen ganin ta aiwatar da su, cikin watanni shiddan da suka rage ma ta a kasafin kudin banan.