Babban Hafsan Sojin Najeriya, Janar Lucky Irabor, ya bayyana cewa laifi ne mutane su dauki makami don kare kai.
Janar Irabo ya bayyana a garin Jos, Jihar Filato cewa doka ta haramta daukar makami don kare kai, saboda ’yan Najeriya su nisanci mallakar makamai don kare kai.
Babban Hafsa Sojin na Najeriya ya yi wannan jawabi ne bayan Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari da takwaransa na Jihar Binuwai, Samuel Ortom, da daidaikun mutane da kungiyoyi sun yi kira ga ’yan Najeriya su tashi su kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga.
Amma Janar Irabo ya ce doka ta haramta daukar makami da sunan kare kai, don haka ’yan Najeriya kar su saba wannan doka.
Ya ce abin da ya kama ta shi ne, “Mutum ya dauki matakan da za su tabbatar yana cikin aminci, ya kuma kawar da duk wani take-take da zai iya maka illa.
“Sannan ka san makwabtanka da halayensu da kuma abin da suke yi, tare da cikakken sanin wurin da kake zaune da abubuwan da ke faruwa a muhallinka.
“Don Allah ku fahimtar da makwabtanku da duk wadanda kuka sani cewa ba sai sun dauki makami za su kare kansu ba.
“Idan an ga wani bakon abu a sanar da jami’an tsaro, amma kare kai ba lallai sai an dauki makami ba. Ba batun mallakar bindigogi ba ne kawai.”