Minista a Ma’aikatar Samar da Ayyuka, Festus Keyamo ya ce Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince a ci gaba da daukar ma’aikata 774,000 domin aiwatar da ayyuka na musamman a kowacce shekara.
Ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake tattaunawa da ayarin ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa a ranar Alhamis.
- Sa-in-sa kan matsalar tsaro: DSS ta gayyaci Sheikh Gumi
- Ana dab da fara cinikin filin jirgin saman Abuja, Kano da wasu guda 2
A yayin kaddamar da shirin dai a watan Janairu, Gwamnatin Tarayya ta ce za a rika dibar matasa 1,000 daga kowacce Karamar Hukuma domin aiwatar da kananan ayyuka a na musamman yankunansu sannan a rika biyan su N1,000 a kowanne wata har tsawon wata uku.
Minista Keyamo ya ce, “Mun amince yanzu aikin zai koma shekara-shekara, tuni ma har mun fara laluben hanyoyin samun kudin aiwatar da shi.
“Wannan ne karon farko da muke aiwatar da irin wannan aikin. Muna bukatar zurfafa tunanin a kai, shi ya sa ma kuke ganin kamar ana jan kafa a farawa. Ba ma so a samu matsala in muka fara.
“Shugaban Kasa da gaske yake yi kan batun tsamo mutum miliyan 100 daga talauci cikin shekara 10 masu zuwa,” inji Keyamo.
A cewar Ministan, ya zuwa 24 ga watan Yunin 2021, akwai kimanin Naira biliyan 24 da aka fitar domin biyan ma’aikata 413,630.
A ranar Alhamis din ta gabata, Aminiya ta rawaito yadda dubban matasan da aka diba domin aikin suka gaza fara karbar albashin nasu.
Ministan ya ce jinkirin ya faru ne saboda matsalar da aka samu wajen daukar bayanan baki na matasan.