✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Aikin DSS: Hattara da masu damfara

DSS ta ce a halin yanzu ba ta fara daukar aiki ba kuma ba ta shafin sada zumunta.

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce ita fa a halin yanzu ba ta daukar ma’aikata sannan ba ta da shafin Facebook.

Jami’in Hulda da Jama’a na DSS, Peter Afunanya, ya bayyana a Abuja ranar Litinin cewa Hukumar ba ta kuma da wasu shafukan sada zumunta.

“Hukumar SSS ba ta daukar aiki sannan ba ta da wani shafin Facebook, hasali ma ba ta da shafuka a kowane dandalin sada zumunta,’’inji shi.

Ya ce, “Muna ankarar da jama’a kan ayyukan damfarar wani mutum mai suna Jesustofunmi Nifemi Alabi, wanda ya bude shafin Facebook mai suna SSS/DSS Recruitment 2019/2020 da niyyar ha’intar masu neman aiki ido rufe.

“Mutumin shi ne Babban Jami’i kuma Shugaban kamfanin Tunrok & Son Nigeria Limited.”

Jami’in ya shawarci masu neman aikin DSS da su tuntubi hedikwatar Hukumar da ke Abuja da sauran ofisoshinta da ke fadin Najeriya da ma shafinta na intanet www.dss.gov.ng  domin sanin ko tana daukar aiki ko akasin haka.