Dan takarar Jam’iyyar PDP, Dauda Lawal-Dare ya ci zaben Gwamnan Jihar Zamfara, inda ya kayar da gwamna mai ci, Bello Muhammad Matawalle da ke neman tazarce.
A wannan Talatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar cewa Dauda Lawal-Dare na ya zama zababben Gwamnan Jihar Zamfara bayan ya samu kuri’u 377,726 daga kananan hukumomi 14 da ke jihar.
- PDP ta ci zaben gwamna a Filato, jihar jagoran yakin zaben Tinubu
- Gwamnatin Kano ta janye dokar hana fita
Baturen zaben da aka gudanar ranar Asabar kuma Shugaban Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi, Farfesa Kassimu Shehu, ya ce Gwamna mai ci Bello Matawalle na APC ne ya zo na biyu a zaben da kuri’u 311,976.
Idan za a iya tunawa, Gwamna Matawalle ya ci zaben wa’adinsa na farko ne a Jam’iyyar PDP, amma daga bisani ya sauya sheka zuwa APC mai mulki a matakin kasa.
Shi dai Dauda Lawal zaben sa a matsayin dan takarar PDP ya kasance mai cike da rudani, inda tun aka yi ta takaddama bayan da ya yi nasara a zaben farko.
Daga baya abokan takararsa suka je kotu, ta soke zaben, ta ba da umarnin a sake wani sabo, amma duk da haka ya sake yin nasara.
Aminiya ta ruwaito cewa kawo yanzu yana cikin jerin sabbin gwamnoni 14 da aka zaba a zaben gwamnonin da aka gudanar a jihohi 28 a Najeriya.
Ga jerin sunayensu, jihohinsu da kuma jihohin:
- Abba Kabir Yusuf (NNPP) — KANO
- Dikko Umar Radda (APC) — KATSINA
- Dauda Lawal Dare (PDP) — ZAMFARA
- Uba Sani (APC) — KADUNA
- Umar Namadi (APC) — JIGAWA
- Umaru Bago (APC) — NEJA
- Ahmad Aliyu (APC) — SAKKWATO
- Caleb Mutfwang (PDP) — FILATO
- Kefas Agbu (PDP) — TARABA
- Bassey Otu (APC) — KUROS RIBA
- Francis Nwifuru (APC) — EBONYI
- Sheriff Oborevwori (PDP) — DELTA
- Umo Eno (PDP) — AKWA IBOM
- Hyacinth Alia (APC) — BINUWAI
- Siminialayi Fubara (PDP) — RIBAS.