✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dauda Dare ne dan takarar gwamnan PDP a Zamfara —Kotun Koli

Hukuncin kotun na zuwa ne kwana hudu kafin zaben gwamnonin jihohi.

Kotun Koli ta tabbatar da Dauda Lawan Dare a matsayin halastaccen dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara.

Hukuncin kotun na zuwa ne kwana hudu kafin zaben gwamnonin jihohin kasar da za a gudanar ranar 11 ga watan Maris.

A hukuncin da suke yanke, alkalan kotun biyar karkashin jagoranci Mai Shari’a Adamu Jauro, duk sun amince da yin watsi da daukaka karar da Dakta Ibrahim Gusau ya shigar gabanta yana kalubalantar takarar Dauda.

Kotun ta ce ta amince da hukuncin kotun Daukaka Kara da ke Sakkwato ta yi ranar 6 ga watan Janairun da muke ciki, wanda ya amince da zaben fitar da gwani na biyu da aka yi wanda a shi ne Dauda Lawan ya yi nasara.

A zaben, Dauda Lawan ya samu nasara da kuri’a 442 a kan abokan takarar tasa.