A ranar Juma’ar da ta gabata ce wani dan ta’addata mai suna Brenton Harrison Tarrant ya kai wani munmunan hari a wasu masallatai biyu da ke garin Christchurch da ke kasar New Zealand inda ya bude wa masallata da ke Sallar Juma’a a masallatan Al-Noor da Linwood wuta ya kashe masallata masu yawa, maza da mata har da yara kanana.
Kwamishinan ’Yan sandan New Zealand Mike Bush ya bayyana a ranar Lahadin da ta gabata cewa dan ta’addan ya kashe mutum 50a masallatan biyu tare da jikkata mutum 50.
Wannan harin da dan ta’addan ya kai ya koyar da darussa masu yawa, babba daga cikinsu shi ne yadda Firayi Ministar Kasar New Zealand, Misis Jacinda Ardern ta nuna kwarewa a shugabanci, domin ta fito fili ta nuna matukar damuwa tare da alhini game da abin da aka yi wa Musulmi, duk da cewa mafi yawan wadanda al’amarin ya shafa ba ’yan asalin kasar ba ne.
Da farko dai Misis Jacinda ta fito ta yi jawabi ga kasar inda ta yi Allah-wadai da abin da ya faru kuma ta kira mutumin da ya aikata laifin da sunan da ya dace da shi, wato dan ta’adda. Sannan ta sanya hijabi ta tafi wurin Musulmi ta jajanta musu kuma ta yi alkawarin biyan kudin da aka kashe a yayin jana’izar wadanda aka kashe, sannan ta ce gwamnati za ta sake fasalin dokar mallakar bindiga a kasar.
Shi dai dan ta’addan yana da lasisin mallakar bindiga mai daraja ta ‘A’ ne wanda ya ba shi damar mallakar bindigogi iri-iri.
Bayan nuna damuwarta a bayyane, Firayi Ministar ta kuma sanya an tura jami’an tsaro Musulmi sun je sun yi wa Musulmi jawabi irin na kwantar da hankali, inda suka nuna musu cewa su ma Musulmi ne gwamnati tana tare da su kuma abin da aka yi bai yi mata dadi ba.
A bangaren ’yan kasar New Zealand kuma, su ma sun fito sun nuna alhini da juyayinsu game da abin da ya faru, inda dubban mutane suka taru a filin wasa na Wellington saboda su nuna rashin goyon bayansu game da abin da dan ta’addan ya aikata.
Haka kuma rahotanni sun nuna cewa sakamakon ta’addancin da dan ta’addan ya aikata mutum 350 ne suka musulunta a kasar ta New Zealand, domin wannan abin ya jawo hankalinsu ga addinin Musulunci.
Sai dai kuma duk da wannan halin karimcin da al’ummar kasar New Zealand suka nuna wa Musulmi a lokacin da suke cikin juyayi, shi kuwa wani Sanatan kasar mai suna Eraser Anning ya dora laifin harin ne a kan Musulmi.
Wani darasin kuma da harin ya fitar shi ne yadda Musulmi suke jajircewa wajen taimaka wa ’yan uwansu ko da za su rasa ransu ne kuwa, domin a wannan ranar an ga yadda limamin masallacin Linwood, daya daga cikin masallatan da aka kai harin, mai suna Imam Alabi Lateef, wanda dan Najeriya ne, ya jajirce wajen ceto rayuka da dama daga cikin masallatan masallacin da yake limanci, maimakon ya gudu ya yi ta kansa.
Babu shakka Firayi Ministar kasar New Zealand Jacinda Ardern ta nuna kwarewa wajen shugabanci domin ta nuna cewa duk wanda yake kasar New Zealand nata ne, kuma duk wanda ya yi ba daidai ba za ta fada, kuma za ta tabbatar an hukunta shi. Sabanin wadansu shugabannin da duk laifin da nasu ya aikata ba su yarda su nuna ya yi laifi sai dai su kare shi. Kuma mutanen kasar New Zealand sun nuna cewa su mutanen kirki ne da suke rungumar kowa da hannu bibbiyu.
Ya kamata wadannan halayen da Firayi Ministar kasar New Zealand da mutanenta suka nuna su zama abin koyi ga shugabannin duniya da kuma sauran jama’a. Domin ba don sun nuna damuwarsu ba da sauran mutanen duniya ba za su bai wa harin muhimmancin da ya samu ba. Idan ana haka za a rage wa ’yan ta’adda kwarin gwiwa domin sun san duniya za ta juya musu baya.
Yanzu dai an kama dan ta’adda Tarrant inda aka gurfanar da shi a gaban kotu ranar Asabar da ta gabata ana tuhumarsa da laifin kisa, ana sa ran zai sake bayyana a kotun ranar 15 ga watan Afrilu, kuma kamar yadda wani jami’i ya bayyana, za a iya kara wasu tuhume-tuhumen a kansa.