Rundunar Sojin Najeriya ta mika mata da kakanan yara 778 da ta damke a samame da ta kai a mafakar ’yan kungiyar Darus Salam a Jihar Nasarawa zuwa jihohinsu.
Mata da kananan yaran su 778, iyalai ne na ’yan kungiyar da suka ranta a na kare bayan sojoji sun tarwatsa sansaninsu a Dajin Uttu da ke Karamar Hukumar Toto ta Jihar a makon jiya.
- Sojoji sun tarwatsa sansanin ‘yan ta’adda a Nasarawa
- Mutanen gari sun cafke masu garkuwa da mutane a Katsina
Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule, ya ce gwamantinsa na fata ’yan kungiyar da suka tsere za su yi amfani da damar da suka samu wajen mika kansu ga hukuma domin sake shigar da su cikin al’umma.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa, Emmanuel Akabe, ya bukaci ’yan kungiyar da suka tsere da su sallama wa gwamnati makamansu domin a samu kwanciyar hankali a jihar da yankin Arewa ta Tsakiya da ma kasa baki daya.
Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Muhammad Ketso, ya karbi ’yan jiharsa daga cikin ’yan Darul Salam din a madadin Gwamna Abubakar Sani Bello.
Jihar Neja ce tafi yawan mutace a cikin wadanda aka kama din da suka hada da mata 86 da kananan yara 232; Sai Jihar Kano mai mata 20 da kananan yara 64.
Ita kuma Jihar Nasarawa na da mata takwas da kananan yara 11 a cikin mutanen.